Sura: Suratul Baqara

Aya : 24

فَإِن لَّمۡ تَفۡعَلُواْ وَلَن تَفۡعَلُواْ فَٱتَّقُواْ ٱلنَّارَ ٱلَّتِي وَقُودُهَا ٱلنَّاسُ وَٱلۡحِجَارَةُۖ أُعِدَّتۡ لِلۡكَٰفِرِينَ

To idan har ba ku aikata hakan ba, kuma ba za ku tava iyawa ba, to ku kiyayi wata wuta wadda mutane ne da duwatsu makamashinta; an kuwa tanade ta domin kafirai



Sura: Suratun Nisa’i

Aya : 56

إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِـَٔايَٰتِنَا سَوۡفَ نُصۡلِيهِمۡ نَارٗا كُلَّمَا نَضِجَتۡ جُلُودُهُم بَدَّلۡنَٰهُمۡ جُلُودًا غَيۡرَهَا لِيَذُوقُواْ ٱلۡعَذَابَۗ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَزِيزًا حَكِيمٗا

Lalle waxanda suka kafirce wa ayoyinmu, za Mu shigar da su wata wuta, duk lokacin da fatunsu suka qone, sai Mu musanya musu da wasu fatun daban, don su xanxani azaba. Lalle Allah Ya kasance Mabuwayi ne, Mai hikima



Sura: Suratul A’araf

Aya : 41

لَهُم مِّن جَهَنَّمَ مِهَادٞ وَمِن فَوۡقِهِمۡ غَوَاشٖۚ وَكَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلظَّـٰلِمِينَ

Suna da shimfixa a cikin Jahannama daga samansu kuma akwai wuta mai lulluve su. Kuma kamar haka ne Muke saka wa azzalumai



Sura: Suratu Yunus

Aya : 27

وَٱلَّذِينَ كَسَبُواْ ٱلسَّيِّـَٔاتِ جَزَآءُ سَيِّئَةِۭ بِمِثۡلِهَا وَتَرۡهَقُهُمۡ ذِلَّةٞۖ مَّا لَهُم مِّنَ ٱللَّهِ مِنۡ عَاصِمٖۖ كَأَنَّمَآ أُغۡشِيَتۡ وُجُوهُهُمۡ قِطَعٗا مِّنَ ٱلَّيۡلِ مُظۡلِمًاۚ أُوْلَـٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلنَّارِۖ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ

Waxanda kuma suka yi mummunan aiki, to sakamakon mummunan aiki irinsa ne, kuma qasqanci zai lulluve su; ba su da wani mai kare su daga (azabar) Allah; kamar dai an lulluve fuskokinsu ne da wani yanki na dare mai duhu qirin. Waxannan su ne ‘yan wuta; su kuma masu dawwama ne a cikinta



Sura: Suratu Hud

Aya : 106

فَأَمَّا ٱلَّذِينَ شَقُواْ فَفِي ٱلنَّارِ لَهُمۡ فِيهَا زَفِيرٞ وَشَهِيقٌ

To waxanda suka tave suna cikin wuta suna ta kururuwa da ihu a cikinta



Sura: Suratu Hud

Aya : 107

خَٰلِدِينَ فِيهَا مَا دَامَتِ ٱلسَّمَٰوَٰتُ وَٱلۡأَرۡضُ إِلَّا مَا شَآءَ رَبُّكَۚ إِنَّ رَبَّكَ فَعَّالٞ لِّمَا يُرِيدُ

Suna madawwama a cikinta matuqar sammai da qasa suna nan a dawwame, sai dai abin da Ubangijinka Ya ga dama. Lalle Ubangijinka Mai yawan aikata abin da Yake nufi ne



Sura: Suratu Ibrahim

Aya : 16

مِّن وَرَآئِهِۦ جَهَنَّمُ وَيُسۡقَىٰ مِن مَّآءٖ صَدِيدٖ

A gabansa Jahannama ce (take jiran sa), za a kuma shayar da shi ruwan mugunya



Sura: Suratu Ibrahim

Aya : 17

يَتَجَرَّعُهُۥ وَلَا يَكَادُ يُسِيغُهُۥ وَيَأۡتِيهِ ٱلۡمَوۡتُ مِن كُلِّ مَكَانٖ وَمَا هُوَ بِمَيِّتٖۖ وَمِن وَرَآئِهِۦ عَذَابٌ غَلِيظٞ

Yana kwankwaxar sa, ba kuwa zai ji daxin haxiyarsa ba, mutuwa kuma za ta zo masa ko ta ina, ba kuwa zai mutu ba; kuma a gabansa ga azaba mai kauri



Sura: Suratu Ibrahim

Aya : 49

وَتَرَى ٱلۡمُجۡرِمِينَ يَوۡمَئِذٖ مُّقَرَّنِينَ فِي ٱلۡأَصۡفَادِ

Kuma za ka ga masu laifi a wannan ranar a ququmce cikin maruruwa



Sura: Suratu Ibrahim

Aya : 50

سَرَابِيلُهُم مِّن قَطِرَانٖ وَتَغۡشَىٰ وُجُوهَهُمُ ٱلنَّارُ

Rigunansu na (tafasasshen) man qaxiran ne[1], kuma wuta za ta lulluve fuskokinsu


1- Qaxiran, wani baqin mai ne kamar kwalta, mai saurin kamawa da wuta, mai kuma xan karen wari.


Sura: Suratul Hijr

Aya : 43

وَإِنَّ جَهَنَّمَ لَمَوۡعِدُهُمۡ أَجۡمَعِينَ

“Lalle kuma Jahannama tabbas makomarsu ce baki xaya



Sura: Suratul Hijr

Aya : 44

لَهَا سَبۡعَةُ أَبۡوَٰبٖ لِّكُلِّ بَابٖ مِّنۡهُمۡ جُزۡءٞ مَّقۡسُومٌ

“Tana da qofofi bakwai, kowacce qofa tana da wani kaso (na kafirai) sananne (da za su shiga ta nan).”



Sura: Suratul Isra’i

Aya : 97

وَمَن يَهۡدِ ٱللَّهُ فَهُوَ ٱلۡمُهۡتَدِۖ وَمَن يُضۡلِلۡ فَلَن تَجِدَ لَهُمۡ أَوۡلِيَآءَ مِن دُونِهِۦۖ وَنَحۡشُرُهُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ عَلَىٰ وُجُوهِهِمۡ عُمۡيٗا وَبُكۡمٗا وَصُمّٗاۖ مَّأۡوَىٰهُمۡ جَهَنَّمُۖ كُلَّمَا خَبَتۡ زِدۡنَٰهُمۡ سَعِيرٗا

Wanda kuwa Allah Ya shiryar to shi ne shiryayye; wanda kuwa Ya vatar to ba za ka sami wani mai taimakon su ba in ban da Shi; za kuma Mu tashe su ranar alqiyama a kan fuskokinsu suna makafi, kurame, bebaye; makomarsu Jahannama; duk sanda ta lafa sai Mu qara musu qunarta



Sura: Suratul Kahf 

Aya : 29

وَقُلِ ٱلۡحَقُّ مِن رَّبِّكُمۡۖ فَمَن شَآءَ فَلۡيُؤۡمِن وَمَن شَآءَ فَلۡيَكۡفُرۡۚ إِنَّآ أَعۡتَدۡنَا لِلظَّـٰلِمِينَ نَارًا أَحَاطَ بِهِمۡ سُرَادِقُهَاۚ وَإِن يَسۡتَغِيثُواْ يُغَاثُواْ بِمَآءٖ كَٱلۡمُهۡلِ يَشۡوِي ٱلۡوُجُوهَۚ بِئۡسَ ٱلشَّرَابُ وَسَآءَتۡ مُرۡتَفَقًا

Kuma ka ce: “Gaskiya daga Ubangijinku take;” to wanda ya ga dama ya yi imani, wanda kuma ya ga dama sai ya kafirta. Lalle kam Mun tanadar wa azzalumai wata wuta wadda katangarta ta kewaye su. Idan kuma suka nemi taimako to za a taimake su ne da ruwa kamar tafasasshen mai da zai riqa toye fuskoki. Tir da wannan abin shan, makoma kuma ta munana



Sura: Suratul Hajji

Aya : 19

۞هَٰذَانِ خَصۡمَانِ ٱخۡتَصَمُواْ فِي رَبِّهِمۡۖ فَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ قُطِّعَتۡ لَهُمۡ ثِيَابٞ مِّن نَّارٖ يُصَبُّ مِن فَوۡقِ رُءُوسِهِمُ ٱلۡحَمِيمُ

Biyu xin nan (muminai da kafirai) masu jayayya ne da suka yi jayayya game da Ubangijinsu (wato addininsu); waxanda suka kafirce sai aka xinka musu tufafi na wuta, kuma ana zuba musu tafasasshen ruwa ta saman kawunansu



Sura: Suratul Hajji

Aya : 20

يُصۡهَرُ بِهِۦ مَا فِي بُطُونِهِمۡ وَٱلۡجُلُودُ

Ana narka abin da yake cikinsu da shi (tafasasshen ruwan) da kuma fatu



Sura: Suratul Hajji

Aya : 21

وَلَهُم مَّقَٰمِعُ مِنۡ حَدِيدٖ

Suna kuma (shan duka) da gudumomi na baqin qarfe



Sura: Suratul Hajji

Aya : 22

كُلَّمَآ أَرَادُوٓاْ أَن يَخۡرُجُواْ مِنۡهَا مِنۡ غَمٍّ أُعِيدُواْ فِيهَا وَذُوقُواْ عَذَابَ ٱلۡحَرِيقِ

Duk sanda suka yi nufin fita daga cikinta (wutar) saboda baqin ciki sai a sake mayar da su cikinta, (a ce da su): “Ku xanxani azabar gobara.”



Sura: Suratul Mu’uminun

Aya : 104

تَلۡفَحُ وُجُوهَهُمُ ٱلنَّارُ وَهُمۡ فِيهَا كَٰلِحُونَ

(Wutar) tana qona fuskokinsu alhali kuwa suna ciccije haqoransu a cikinta



Sura: Suratul Furqan

Aya : 12

إِذَا رَأَتۡهُم مِّن مَّكَانِۭ بَعِيدٖ سَمِعُواْ لَهَا تَغَيُّظٗا وَزَفِيرٗا

Idan (wutar) ta hango su daga wuri mai nisa sai su ji tafarfasa da gurnaninta



Sura: Suratul Furqan

Aya : 13

وَإِذَآ أُلۡقُواْ مِنۡهَا مَكَانٗا ضَيِّقٗا مُّقَرَّنِينَ دَعَوۡاْ هُنَالِكَ ثُبُورٗا

Idan kuwa aka jefa su cikinta a wani wuri quntatacce nata, suna ququnce, sai su riqa kiran hallaka a can



Sura: Suratul Ahzab

Aya : 66

يَوۡمَ تُقَلَّبُ وُجُوهُهُمۡ فِي ٱلنَّارِ يَقُولُونَ يَٰلَيۡتَنَآ أَطَعۡنَا ٱللَّهَ وَأَطَعۡنَا ٱلرَّسُولَا۠

A ranar da za a riqa jujjuya fuskokinsu cikin wuta, suna cewa: “Kaiconmu, ina ma da mun bi Allah mun bi Manzo!”



Sura: Suratu Sad

Aya : 56

جَهَنَّمَ يَصۡلَوۡنَهَا فَبِئۡسَ ٱلۡمِهَادُ

(Wato) Jahannama wadda za su shige ta, to wannan shimfixar zama ta munana



Sura: Suratu Sad

Aya : 57

هَٰذَا فَلۡيَذُوقُوهُ حَمِيمٞ وَغَسَّاقٞ

Wannan (sakamako ne), sai su xanxane shi na tafasasshen ruwa da mugunya



Sura: Suratu Sad

Aya : 58

وَءَاخَرُ مِن شَكۡلِهِۦٓ أَزۡوَٰجٌ

Da kuma wani mai kama da shi iri daban-daban



Sura: Suratuz Zumar

Aya : 16

لَهُم مِّن فَوۡقِهِمۡ ظُلَلٞ مِّنَ ٱلنَّارِ وَمِن تَحۡتِهِمۡ ظُلَلٞۚ ذَٰلِكَ يُخَوِّفُ ٱللَّهُ بِهِۦ عِبَادَهُۥۚ يَٰعِبَادِ فَٱتَّقُونِ

Suna da inuwoyi na wuta a samansu, a qarqashinsu kuma akwai wasu inuwoyin. Wannan ne fa Allah Yake tsoratar da bayinsa da shi. Ya ku bayina, sai ku kiyaye dokokina



Sura: Suratuz Zumar

Aya : 72

قِيلَ ٱدۡخُلُوٓاْ أَبۡوَٰبَ جَهَنَّمَ خَٰلِدِينَ فِيهَاۖ فَبِئۡسَ مَثۡوَى ٱلۡمُتَكَبِّرِينَ

Aka ce: “Ku shiga qofofin Jahannama, kuna masu dawwama a cikinta;” to makomar masu girman kai ta munana



Sura: Suratu Ghafir

Aya : 70

ٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِٱلۡكِتَٰبِ وَبِمَآ أَرۡسَلۡنَا بِهِۦ رُسُلَنَاۖ فَسَوۡفَ يَعۡلَمُونَ

(Su ne) waxanda suka qaryata Alqur’ani da kuma abin da Muka aiko manzanninmu da shi; to ba da daxewa ba za su sani



Sura: Suratu Ghafir

Aya : 71

إِذِ ٱلۡأَغۡلَٰلُ فِيٓ أَعۡنَٰقِهِمۡ وَٱلسَّلَٰسِلُ يُسۡحَبُونَ

A yayin da ququmai suke a wuyoyinsu, da kuma sarqoqi ana jan su



Sura: Suratu Ghafir

Aya : 72

فِي ٱلۡحَمِيمِ ثُمَّ فِي ٱلنَّارِ يُسۡجَرُونَ

A cikin tafasasshen ruwan, sannan kuma ana qona su a cikin wuta