Sura: Suratul Baqara

Aya : 42

وَلَا تَلۡبِسُواْ ٱلۡحَقَّ بِٱلۡبَٰطِلِ وَتَكۡتُمُواْ ٱلۡحَقَّ وَأَنتُمۡ تَعۡلَمُونَ

Kada kuma ku gauraya gaskiya da qarya, kuma ku voye gaskiya, alhalin kuna sane



Sura: Suratul Baqara

Aya : 140

أَمۡ تَقُولُونَ إِنَّ إِبۡرَٰهِـۧمَ وَإِسۡمَٰعِيلَ وَإِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَ وَٱلۡأَسۡبَاطَ كَانُواْ هُودًا أَوۡ نَصَٰرَىٰۗ قُلۡ ءَأَنتُمۡ أَعۡلَمُ أَمِ ٱللَّهُۗ وَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّن كَتَمَ شَهَٰدَةً عِندَهُۥ مِنَ ٱللَّهِۗ وَمَا ٱللَّهُ بِغَٰفِلٍ عَمَّا تَعۡمَلُونَ

Ko kuma kuna cewa ne, “Lalle Ibrahimu da Isma’ila da Ishaqa da Ya’aqubu da jikoki sun kasance Yahudawa ne ko Nasara?” Ka ce: “Ku ne kuka fi sani ko kuma Allah?” Kuma ba wanda ya fi zalunci kamar wanda ya voye shaidar da take wajensa daga Allah, kuma Allah ba rafkananne ne ba game da abin da kuke aikatawa



Sura: Suratul Baqara

Aya : 159

إِنَّ ٱلَّذِينَ يَكۡتُمُونَ مَآ أَنزَلۡنَا مِنَ ٱلۡبَيِّنَٰتِ وَٱلۡهُدَىٰ مِنۢ بَعۡدِ مَا بَيَّنَّـٰهُ لِلنَّاسِ فِي ٱلۡكِتَٰبِ أُوْلَـٰٓئِكَ يَلۡعَنُهُمُ ٱللَّهُ وَيَلۡعَنُهُمُ ٱللَّـٰعِنُونَ

Lalle waxanda suke voye abin da Muka saukar na hujjoji da shiriya bayan Mun yi bayanin su ga mutane a cikin Littafi, to waxannan su ne Allah Yake la’antar su, kuma masu la’anta su ma suke la’antar su



Sura: Suratul Baqara

Aya : 174

إِنَّ ٱلَّذِينَ يَكۡتُمُونَ مَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ مِنَ ٱلۡكِتَٰبِ وَيَشۡتَرُونَ بِهِۦ ثَمَنٗا قَلِيلًا أُوْلَـٰٓئِكَ مَا يَأۡكُلُونَ فِي بُطُونِهِمۡ إِلَّا ٱلنَّارَ وَلَا يُكَلِّمُهُمُ ٱللَّهُ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ وَلَا يُزَكِّيهِمۡ وَلَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٌ

Lalle waxanda suke voye abin da Allah Ya saukar na Littafi, kuma suke musanya shi da xan kuxi kaxan, waxannan babu abin da suke ci a cikkunansu sai wuta, kuma Allah ba zai yi musu magana ba ranar tashin alqiyama, kuma ba zai tsarkake su ba, kuma suna da wata azaba mai raxaxi



Sura: Suratu Ali-Imran

Aya : 137

قَدۡ خَلَتۡ مِن قَبۡلِكُمۡ سُنَنٞ فَسِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَٱنظُرُواْ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلۡمُكَذِّبِينَ

Haqiqa sunnoni (na Allah) sun riga sun shuxe gabaninku, to sai ku yi tafiya cikin qasa, sai ku duba ku ga yaya qarshen masu qaryatawa ya zama?



Sura: Suratu Ali-Imran

Aya : 187

وَإِذۡ أَخَذَ ٱللَّهُ مِيثَٰقَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ لَتُبَيِّنُنَّهُۥ لِلنَّاسِ وَلَا تَكۡتُمُونَهُۥ فَنَبَذُوهُ وَرَآءَ ظُهُورِهِمۡ وَٱشۡتَرَوۡاْ بِهِۦ ثَمَنٗا قَلِيلٗاۖ فَبِئۡسَ مَا يَشۡتَرُونَ

Kuma ka tuna lokacin da Allah Ya xauki alqawari daga waxanda aka bai wa Littafi cewa: “Lalle ku bayyana shi ga mutane, kuma kada ku voye shi.” Sai suka jefar da shi can bayansu, kuma suka musanya shi da wani xan farashi qanqani. To tir da abin da suke yin musanye da shi



Sura: Suratul An’am

Aya : 11

قُلۡ سِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ ثُمَّ ٱنظُرُواْ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلۡمُكَذِّبِينَ

Ka ce: “Ku yi tafiya a bayan qasa, sannan ku duba ku ga, yaya qarshen lamarin masu qaryatawa ya kasance?”



Sura: Suratul An’am

Aya : 99

وَهُوَ ٱلَّذِيٓ أَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَأَخۡرَجۡنَا بِهِۦ نَبَاتَ كُلِّ شَيۡءٖ فَأَخۡرَجۡنَا مِنۡهُ خَضِرٗا نُّخۡرِجُ مِنۡهُ حَبّٗا مُّتَرَاكِبٗا وَمِنَ ٱلنَّخۡلِ مِن طَلۡعِهَا قِنۡوَانٞ دَانِيَةٞ وَجَنَّـٰتٖ مِّنۡ أَعۡنَابٖ وَٱلزَّيۡتُونَ وَٱلرُّمَّانَ مُشۡتَبِهٗا وَغَيۡرَ مُتَشَٰبِهٍۗ ٱنظُرُوٓاْ إِلَىٰ ثَمَرِهِۦٓ إِذَآ أَثۡمَرَ وَيَنۡعِهِۦٓۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكُمۡ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يُؤۡمِنُونَ

Kuma Shi ne Wanda Ya saukar da ruwa daga sama, sai Muka fitar da kowane irin dangin tsiro da shi, sannan Muka fitar da shi (tsiron) (wasu) koraye, daga gare shi kuma Muke fitar da qwayoyi a cunkushe daga gare shi. Kuma daga hudar dabino (ake samun) nonuna waxanda suke dab da qasa; da kuma waxansu lambuna na inabi da zaitun da ruman, masu kama da juna da kuma mabambanta. Ku kalli ‘ya’yansu idan suka yi ‘ya’ya da kuma lokacin da suka nuna. Lalle game da wannan akwai ayoyi ga mutanen da suka yi imani



Sura: Suratul A’araf

Aya : 86

وَلَا تَقۡعُدُواْ بِكُلِّ صِرَٰطٖ تُوعِدُونَ وَتَصُدُّونَ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ مَنۡ ءَامَنَ بِهِۦ وَتَبۡغُونَهَا عِوَجٗاۚ وَٱذۡكُرُوٓاْ إِذۡ كُنتُمۡ قَلِيلٗا فَكَثَّرَكُمۡۖ وَٱنظُرُواْ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلۡمُفۡسِدِينَ

“Kuma kada ku zauna a kan kowace hanya kuna tsoratar da (mutane), kuma kuna toshe hanyar Allah ga duk wanda ya yi imani da Shi, kuna kuma son ta zama karkatacciya. Kuma ku tuna (ni’imar Allah) lokacin da kuke ‘yan kaxan, sai Ya yawaita ku, kuma ku duba ku ga yaya qarshen mavarnata ya kasance?



Sura: Suratul A’araf

Aya : 185

أَوَلَمۡ يَنظُرُواْ فِي مَلَكُوتِ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا خَلَقَ ٱللَّهُ مِن شَيۡءٖ وَأَنۡ عَسَىٰٓ أَن يَكُونَ قَدِ ٱقۡتَرَبَ أَجَلُهُمۡۖ فَبِأَيِّ حَدِيثِۭ بَعۡدَهُۥ يُؤۡمِنُونَ

Shin ba za su yi duba cikin mulkin sammai da qasa da kuma abin da Allah Ya halitta ba, kuma lalle ya kusata a ce ajalinsu yana gab da zuwa, to da wane zance ne za su yi imani bayansa (wato Alqur’ani)?



Sura: Suratut Tauba

Aya : 122

۞وَمَا كَانَ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ لِيَنفِرُواْ كَآفَّةٗۚ فَلَوۡلَا نَفَرَ مِن كُلِّ فِرۡقَةٖ مِّنۡهُمۡ طَآئِفَةٞ لِّيَتَفَقَّهُواْ فِي ٱلدِّينِ وَلِيُنذِرُواْ قَوۡمَهُمۡ إِذَا رَجَعُوٓاْ إِلَيۡهِمۡ لَعَلَّهُمۡ يَحۡذَرُونَ

Bai kamata muminai su fita yaqi gaba xaya ba. Me zai hana wasu jama’a daga kowace qabila (su zauna) don su koyi ilimin addini, su kuma yi wa mutanensu gargaxi idan sun dawo musu don su kiyaye (dokokin Allah)?



Sura: Suratu Yunus

Aya : 101

قُلِ ٱنظُرُواْ مَاذَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ وَمَا تُغۡنِي ٱلۡأٓيَٰتُ وَٱلنُّذُرُ عَن قَوۡمٖ لَّا يُؤۡمِنُونَ

Ka ce: “Ku yi tunanin abubuwan da suke cikin sammai da qasa.” Ayoyi kuwa da masu gargaxi ba sa wadatar da mutanen da ba sa yin imani



Sura: Suratu Yusuf 

Aya : 109

وَمَآ أَرۡسَلۡنَا مِن قَبۡلِكَ إِلَّا رِجَالٗا نُّوحِيٓ إِلَيۡهِم مِّنۡ أَهۡلِ ٱلۡقُرَىٰٓۗ أَفَلَمۡ يَسِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَيَنظُرُواْ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۗ وَلَدَارُ ٱلۡأٓخِرَةِ خَيۡرٞ لِّلَّذِينَ ٱتَّقَوۡاْۚ أَفَلَا تَعۡقِلُونَ

Ba Mu kuma aiko (manzanni) a gabaninka ba sai maza ‘yan birni waxanda Muke yi wa wahayi. Me ya sa (kafirai) ba za su yi tafiya ba a bayan qasa don su ga yadda qarshen waxanda suka rigaye su ya kasance? Lalle kuwa gidan lahira shi ya fi ga waxanda suke kiyaye dokokin (Allah). Shin ba za ku hankalta ba?



Sura: Suratun Nahl

Aya : 36

وَلَقَدۡ بَعَثۡنَا فِي كُلِّ أُمَّةٖ رَّسُولًا أَنِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ وَٱجۡتَنِبُواْ ٱلطَّـٰغُوتَۖ فَمِنۡهُم مَّنۡ هَدَى ٱللَّهُ وَمِنۡهُم مَّنۡ حَقَّتۡ عَلَيۡهِ ٱلضَّلَٰلَةُۚ فَسِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَٱنظُرُواْ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلۡمُكَذِّبِينَ

Haqiqa kuma Mun aiko manzo a kowacce al’umma cewa,: “Ku bauta wa Allah, kuma ku nisanci Xagutu[1].” To akwai daga cikinsu waxanda Allah Ya shiryar, akwai kuma daga cikinsu wanda vata ya tabbata a kansa. To ku yi tafiya a bayan qasa ku ga yadda qarshen masu qaryatawa ya kasance


1- Xagutu ana nufin duk wani abu da aka qetare iyakokin Allah saboda shi, ta hanyar bautar sa, mutum ne ko aljani ko dutse ko itace.


Sura: Suratun Nahl

Aya : 43

وَمَآ أَرۡسَلۡنَا مِن قَبۡلِكَ إِلَّا رِجَالٗا نُّوحِيٓ إِلَيۡهِمۡۖ فَسۡـَٔلُوٓاْ أَهۡلَ ٱلذِّكۡرِ إِن كُنتُمۡ لَا تَعۡلَمُونَ

Ba Mu tava aiko (wasu manzanni) ba a gabaninka sai mazaje waxanda Muke yi wa wahayi. Don haka ku tambayi ma’abota ilimi idan kun kasance ba ku sani ba



Sura: Suratun Nahl

Aya : 44

بِٱلۡبَيِّنَٰتِ وَٱلزُّبُرِۗ وَأَنزَلۡنَآ إِلَيۡكَ ٱلذِّكۡرَ لِتُبَيِّنَ لِلنَّاسِ مَا نُزِّلَ إِلَيۡهِمۡ وَلَعَلَّهُمۡ يَتَفَكَّرُونَ

(Mun aiko su) da hujjoji bayyanannu da littattafai. Mun kuma saukar maka da Alqur’ani don ka yi wa mutane bayanin abin da aka saukar musu ko sa yi tunani



Sura: Suratu Xa Ha

Aya : 114

فَتَعَٰلَى ٱللَّهُ ٱلۡمَلِكُ ٱلۡحَقُّۗ وَلَا تَعۡجَلۡ بِٱلۡقُرۡءَانِ مِن قَبۡلِ أَن يُقۡضَىٰٓ إِلَيۡكَ وَحۡيُهُۥۖ وَقُل رَّبِّ زِدۡنِي عِلۡمٗا

Kuma fa Allah Sarki na gaskiya Ya xaukaka (daga maganganun kafirai). Kada kuma ka yi garaje da (karatun) Alqur’ani tun kafin a gama yi maka wahayinsa, kuma ka ce: “Ubangiji Ka qara min ilimi.”



Sura: Suratul Furqan

Aya : 59

ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ وَمَا بَيۡنَهُمَا فِي سِتَّةِ أَيَّامٖ ثُمَّ ٱسۡتَوَىٰ عَلَى ٱلۡعَرۡشِۖ ٱلرَّحۡمَٰنُ فَسۡـَٔلۡ بِهِۦ خَبِيرٗا

(Shi ne) wanda Ya halicci sammai da qasa da abin da yake tsakaninsu cikin kwana shida, sannan Ya daidaita a kan Al’arshi. (Shi ne) Arrahmanu, sai ka tambayi Masani game da Shi



Sura: Suratul Qasas

Aya : 69

وَرَبُّكَ يَعۡلَمُ مَا تُكِنُّ صُدُورُهُمۡ وَمَا يُعۡلِنُونَ

Kuma Ubangijinka Ya san abin da zukatansu suke voyewa da kuma abin da suke bayyanawa



Sura: Suratul Ankabut

Aya : 20

قُلۡ سِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَٱنظُرُواْ كَيۡفَ بَدَأَ ٱلۡخَلۡقَۚ ثُمَّ ٱللَّهُ يُنشِئُ ٱلنَّشۡأَةَ ٱلۡأٓخِرَةَۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ

Ka ce: “Ku yi tafiya a bayan qasa sai ku duba ku ga yadda Allah Ya fari halittu. Sannan Allah ne zai sake samar da su samarwar qarshe. Lalle Allah Mai iko ne a kan komai



Sura: Suratur Rum

Aya : 9

أَوَلَمۡ يَسِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَيَنظُرُواْ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۚ كَانُوٓاْ أَشَدَّ مِنۡهُمۡ قُوَّةٗ وَأَثَارُواْ ٱلۡأَرۡضَ وَعَمَرُوهَآ أَكۡثَرَ مِمَّا عَمَرُوهَا وَجَآءَتۡهُمۡ رُسُلُهُم بِٱلۡبَيِّنَٰتِۖ فَمَا كَانَ ٱللَّهُ لِيَظۡلِمَهُمۡ وَلَٰكِن كَانُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ يَظۡلِمُونَ

Shin ba za su yi tafiya a bayan qasa ba su ga yadda qarshen waxanda suka gabace su ya zama? Sun kasance sun fi su tsananin qarfi, sun kuma tona qasa suka kuma raya ta fiye da yadda su (mutanen Makka) suka raya ta, kuma manzanninsu sun zo musu da (ayoyi) bayyanannu; to Allah bai kasance Mai zaluntar su ba, sai dai su ne suka kasance suna zaluntar kawunansu



Sura: Suratur Rum

Aya : 42

قُلۡ سِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَٱنظُرُواْ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلُۚ كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّشۡرِكِينَ

Ka ce (da su): “Ku yi tafiya mana a bayan qasa sannan ku duba ku ga yadda qarshen waxanda suke gabaninku ya zama. Yawancinsu sun kasance mushirikai



Sura: Suratu Faxir

Aya : 44

أَوَلَمۡ يَسِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَيَنظُرُواْ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡ وَكَانُوٓاْ أَشَدَّ مِنۡهُمۡ قُوَّةٗۚ وَمَا كَانَ ٱللَّهُ لِيُعۡجِزَهُۥ مِن شَيۡءٖ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَلَا فِي ٱلۡأَرۡضِۚ إِنَّهُۥ كَانَ عَلِيمٗا قَدِيرٗا

Shin ba su yi tafiya ba ne a cikin qasa, sai su ga yaya qarshen waxanda suke gabaninsu ya kasance, alhali kuwa sun zamanto qarfafa fiye da su? Ba kuwa wani abu da zai gagari Allah a cikin sammai ko a cikin qasa. Lalle Shi Ya kasance Masani ne, Mai iko



Sura: Suratuz Zumar

Aya : 9

أَمَّنۡ هُوَ قَٰنِتٌ ءَانَآءَ ٱلَّيۡلِ سَاجِدٗا وَقَآئِمٗا يَحۡذَرُ ٱلۡأٓخِرَةَ وَيَرۡجُواْ رَحۡمَةَ رَبِّهِۦۗ قُلۡ هَلۡ يَسۡتَوِي ٱلَّذِينَ يَعۡلَمُونَ وَٱلَّذِينَ لَا يَعۡلَمُونَۗ إِنَّمَا يَتَذَكَّرُ أُوْلُواْ ٱلۡأَلۡبَٰبِ

Shin yanzu wanda yake shi mai ibada ne a cikin sa’o’in dare, yana sujjada yana kuma tsayawa, yana tsoron ranar lahira yana kuma qaunar rahamar Ubangijinsa (zai yi daidai da wanda ba haka yake ba?) Ka ce: “Yanzu waxanda suke da sani za su yi daidai da waxanda ba su da sani? Ma’abota hankula ne kawai suke wa’azantuwa



Sura: Suratu Ghafir

Aya : 21

۞أَوَلَمۡ يَسِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَيَنظُرُواْ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلَّذِينَ كَانُواْ مِن قَبۡلِهِمۡۚ كَانُواْ هُمۡ أَشَدَّ مِنۡهُمۡ قُوَّةٗ وَءَاثَارٗا فِي ٱلۡأَرۡضِ فَأَخَذَهُمُ ٱللَّهُ بِذُنُوبِهِمۡ وَمَا كَانَ لَهُم مِّنَ ٱللَّهِ مِن وَاقٖ

Shin ba sa tafiya a bayan qasa sannan su ga yaya qarshen waxanda suka kasance gabaninsu ya zama? Su sun kasance sun fi su tsananin qarfi da barin gurabe na tarihi a bayan qasa, sai Allah Ya kama su da laifukansu, ba su kuma da wani mai kare su daga Allah



Sura: Suratu Ghafir

Aya : 82

أَفَلَمۡ يَسِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَيَنظُرُواْ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۚ كَانُوٓاْ أَكۡثَرَ مِنۡهُمۡ وَأَشَدَّ قُوَّةٗ وَءَاثَارٗا فِي ٱلۡأَرۡضِ فَمَآ أَغۡنَىٰ عَنۡهُم مَّا كَانُواْ يَكۡسِبُونَ

Shin ba za su yi tafiya ba a bayan qasa sannan su duba yadda qarshen waxanda suke gabaninsu ya zama? Sun zamanto sun fi su yawa, sun kuma fi su tsananin qarfi da barin gurabe a bayan qasa; to abin da suka kasance suna aikatawa bai wadatar musu da komai ba



Sura: Suratu Muhammad

Aya : 10

۞أَفَلَمۡ يَسِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَيَنظُرُواْ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۖ دَمَّرَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِمۡۖ وَلِلۡكَٰفِرِينَ أَمۡثَٰلُهَا

Yanzu ba za su yi tafiya a bayan qasa ba sai su duba yaya qarshen waxanda suka gabace su ya kasance? Allah Ya hallaka su; kafirai kuma suna da (sakamako) kwatankwacinsa



Sura: Suratu Qaf 

Aya : 6

أَفَلَمۡ يَنظُرُوٓاْ إِلَى ٱلسَّمَآءِ فَوۡقَهُمۡ كَيۡفَ بَنَيۡنَٰهَا وَزَيَّنَّـٰهَا وَمَا لَهَا مِن فُرُوجٖ

Yanzu ba sa duban sama da take sama da su (su ga) yadda Muka gina ta, Muka kuma qawata ta, ba ta kuma da wasu tsage-tsage?



Sura: Suratul Mujadila

Aya : 11

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا قِيلَ لَكُمۡ تَفَسَّحُواْ فِي ٱلۡمَجَٰلِسِ فَٱفۡسَحُواْ يَفۡسَحِ ٱللَّهُ لَكُمۡۖ وَإِذَا قِيلَ ٱنشُزُواْ فَٱنشُزُواْ يَرۡفَعِ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مِنكُمۡ وَٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡعِلۡمَ دَرَجَٰتٖۚ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ خَبِيرٞ

Ya ku waxanda suka yi imani, idan aka ce da ku: “Ku yalwata a wuraren zama,” to sai ku yalwata, Allah zai yalwata muku[1]; idan kuma aka ce: “Ku tashi (daga wurinku)[2],” to sai ku tashi, Allah zai xaga darajojin waxanda suka yi imani daga cikinku da waxanda aka bai wa ilimi. Allah kuma Masanin abin da kuke aikatawa ne


1- Watau zai buxa musu a rayuwarsu ta duniya da ta lahira.


2- Watau domin wani aiki na addini ko wata buqata da ta taso.


Sura: Suratu Abasa

Aya : 24

فَلۡيَنظُرِ ٱلۡإِنسَٰنُ إِلَىٰ طَعَامِهِۦٓ

To mutum ya yi duba zuwa ga abincinsa mana?