Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 57

فَأَخۡرَجۡنَٰهُم مِّن جَنَّـٰتٖ وَعُيُونٖ

(Allah Ya ce): Sai Muka fitar da su daga gonaki da kuma idandunan ruwa



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 58

وَكُنُوزٖ وَمَقَامٖ كَرِيمٖ

Da taskoki da kuma mazauni na alfarma



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 59

كَذَٰلِكَۖ وَأَوۡرَثۡنَٰهَا بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ

Kamar haka ne Muka gadar da su ga Banu-Isra’ila



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 60

فَأَتۡبَعُوهُم مُّشۡرِقِينَ

Sai suka bi bayansu a lokacin fitowar rana



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 61

فَلَمَّا تَرَـٰٓءَا ٱلۡجَمۡعَانِ قَالَ أَصۡحَٰبُ مُوسَىٰٓ إِنَّا لَمُدۡرَكُونَ

To lokacin da jama’ar biyu suka ga juna, sai sahabban Musa suka ce: “Lalle tabbas mu za a cim mana.”



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 62

قَالَ كَلَّآۖ إِنَّ مَعِيَ رَبِّي سَيَهۡدِينِ

(Musa) ya ce: “A’a; Ubangijina Yana tare da ni, zai kuwa shiryar da ni (hanyar tsira).”



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 63

فَأَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰ مُوسَىٰٓ أَنِ ٱضۡرِب بِّعَصَاكَ ٱلۡبَحۡرَۖ فَٱنفَلَقَ فَكَانَ كُلُّ فِرۡقٖ كَٱلطَّوۡدِ ٱلۡعَظِيمِ

Sai Muka yi wahayi ga Musa cewa: “Ka bugi kogin da sandarka;” (da ya buge shi) sai ya dare, kowanne yanki sai ya zama kamar qaton dutse



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 64

وَأَزۡلَفۡنَا ثَمَّ ٱلۡأٓخَرِينَ

Muka kuma kusantar da waxancan (watau mutanen Fir’auna) zuwa can (kusa da kogin)



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 65

وَأَنجَيۡنَا مُوسَىٰ وَمَن مَّعَهُۥٓ أَجۡمَعِينَ

Muka kuma tserar da Musa da waxanda suke tare da shi gaba xaya



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 66

ثُمَّ أَغۡرَقۡنَا ٱلۡأٓخَرِينَ

Sannan Muka nutsar da sauran mutanen (watau Fir’auna da mutanensa)



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 67

إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ

Lalle a game da wannan tabbas akwai aya; kuma yawancinsu ba su zamanto muminai ba



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 68

وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ

Kuma lalle Ubangijika tabbas Shi Mabuwayi ne, Mai rahama



Sura: Suratul Qasas

Aya : 3

نَتۡلُواْ عَلَيۡكَ مِن نَّبَإِ مُوسَىٰ وَفِرۡعَوۡنَ بِٱلۡحَقِّ لِقَوۡمٖ يُؤۡمِنُونَ

Muna karanta maka labarin Musa da Fir’auna da gaskiya don mutane da suke yin imani



Sura: Suratul Qasas

Aya : 4

إِنَّ فِرۡعَوۡنَ عَلَا فِي ٱلۡأَرۡضِ وَجَعَلَ أَهۡلَهَا شِيَعٗا يَسۡتَضۡعِفُ طَآئِفَةٗ مِّنۡهُمۡ يُذَبِّحُ أَبۡنَآءَهُمۡ وَيَسۡتَحۡيِۦ نِسَآءَهُمۡۚ إِنَّهُۥ كَانَ مِنَ ٱلۡمُفۡسِدِينَ

Lalle Fir’auna ya yi xagawa a cikin qasar (Masar) ya kuma mayar da mutanenta qungiyoyi daban-daban, yana bautar da wata qungiyar daga cikinsu, yana yanka ‘ya’yayensu maza, yana kuma qyale matansu da rai. Lalle shi ya kasance cikin mavarnata



Sura: Suratul Qasas

Aya : 5

وَنُرِيدُ أَن نَّمُنَّ عَلَى ٱلَّذِينَ ٱسۡتُضۡعِفُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَنَجۡعَلَهُمۡ أَئِمَّةٗ وَنَجۡعَلَهُمُ ٱلۡوَٰرِثِينَ

Muna kuma nufin za Mu yi baiwa ga waxanda aka wulaqanta a cikin qasar (Masar) Mu kuma mayar da su shugabanni, kuma Mu mayar da su magadan (mulkin Fir’auna)



Sura: Suratul Qasas

Aya : 6

وَنُمَكِّنَ لَهُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَنُرِيَ فِرۡعَوۡنَ وَهَٰمَٰنَ وَجُنُودَهُمَا مِنۡهُم مَّا كَانُواْ يَحۡذَرُونَ

Mu kuma kafa su a qasar, kuma Mu nuna wa Fir’auna da Hamana da rundunoninsu gaba xayansu abin da suke jin tsoro game da su (Banu Isra’ila)



Sura: Suratul Qasas

Aya : 7

وَأَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰٓ أُمِّ مُوسَىٰٓ أَنۡ أَرۡضِعِيهِۖ فَإِذَا خِفۡتِ عَلَيۡهِ فَأَلۡقِيهِ فِي ٱلۡيَمِّ وَلَا تَخَافِي وَلَا تَحۡزَنِيٓۖ إِنَّا رَآدُّوهُ إِلَيۡكِ وَجَاعِلُوهُ مِنَ ٱلۡمُرۡسَلِينَ

Muka kuma yi wa mahaifiyar Musa wahayi da cewa: “Ki shayar da shi; to yayin da kika ji masa tsoro, sai ki jefa shi a cikin kogi, kada kuma ki ji tsoro, kuma kada ki yi baqin ciki; lalle Mu Masu dawo miki da shi ne, kuma Masu sanya shi ne cikin manzanni.”



Sura: Suratul Qasas

Aya : 8

فَٱلۡتَقَطَهُۥٓ ءَالُ فِرۡعَوۡنَ لِيَكُونَ لَهُمۡ عَدُوّٗا وَحَزَنًاۗ إِنَّ فِرۡعَوۡنَ وَهَٰمَٰنَ وَجُنُودَهُمَا كَانُواْ خَٰطِـِٔينَ

Sai mutanen Fir’auna suka tsince shi domin (daga baya) ya zama abokin gaba da kuma baqin ciki a gare su. Lalle Fir’auna da Hamana da rundunoninsu sun kasance masu laifi



Sura: Suratul Qasas

Aya : 9

وَقَالَتِ ٱمۡرَأَتُ فِرۡعَوۡنَ قُرَّتُ عَيۡنٖ لِّي وَلَكَۖ لَا تَقۡتُلُوهُ عَسَىٰٓ أَن يَنفَعَنَآ أَوۡ نَتَّخِذَهُۥ وَلَدٗا وَهُمۡ لَا يَشۡعُرُونَ

Matar Fir’auna kuma ta ce: “(Shi) farin ciki ne a gare ni har da kai; kada ku kashe shi, muna fatan ya amfane mu ko kuma mu xauke shi a matsayin xa,” alhali kuwa su ba su san (abin da zai faru ba)



Sura: Suratul Qasas

Aya : 10

وَأَصۡبَحَ فُؤَادُ أُمِّ مُوسَىٰ فَٰرِغًاۖ إِن كَادَتۡ لَتُبۡدِي بِهِۦ لَوۡلَآ أَن رَّبَطۡنَا عَلَىٰ قَلۡبِهَا لِتَكُونَ مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ

Zuciyar mahaifiyar Musa kuma ta wayi gari ba komai a cikinta (sai tunaninsa); ba shakka sauran qiris ta bayyana shi, ba don Mun xaure zuciyarta ba don ta zama cikin muminai



Sura: Suratul Qasas

Aya : 11

وَقَالَتۡ لِأُخۡتِهِۦ قُصِّيهِۖ فَبَصُرَتۡ بِهِۦ عَن جُنُبٖ وَهُمۡ لَا يَشۡعُرُونَ

Ta kuma ce da ‘yar’uwarsa: “Ki bi sawunsa”; sai ta hango shi daga nesa, su kuwa ba su gane ita (‘yar’uwarsa ba ce)



Sura: Suratul Qasas

Aya : 12

۞وَحَرَّمۡنَا عَلَيۡهِ ٱلۡمَرَاضِعَ مِن قَبۡلُ فَقَالَتۡ هَلۡ أَدُلُّكُمۡ عَلَىٰٓ أَهۡلِ بَيۡتٖ يَكۡفُلُونَهُۥ لَكُمۡ وَهُمۡ لَهُۥ نَٰصِحُونَ

Da ma kuma can Mun haramta masa (nonon) masu shayarwa[1], sai (‘yar’uwar tasa) ta ce: “Yanzu ba na nuna muku mutanen wani gida da za su shayar muku da shi ba, su kuma za su kyautata masa?”


1- Watau ya qi karvar nonon duk wata mai shayarwa da aka kawo don shayar da shi a gidan Fir’auna.


Sura: Suratul Qasas

Aya : 13

فَرَدَدۡنَٰهُ إِلَىٰٓ أُمِّهِۦ كَيۡ تَقَرَّ عَيۡنُهَا وَلَا تَحۡزَنَ وَلِتَعۡلَمَ أَنَّ وَعۡدَ ٱللَّهِ حَقّٞ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ

Sai Muka dawo da shi wurin mahaifiyarsa don hankalinta ya kwanta kuma don kada ta yi baqin ciki, don kuma ta san cewa alqawarin Allah gaskiya ne, sai dai kuma yawancinsu ba sa fahimtar (haka)



Sura: Suratul Qasas

Aya : 14

وَلَمَّا بَلَغَ أَشُدَّهُۥ وَٱسۡتَوَىٰٓ ءَاتَيۡنَٰهُ حُكۡمٗا وَعِلۡمٗاۚ وَكَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ

Lokacin kuma da ya kai ganiyar qarfinsa ya kuma kammala, sai Muka ba shi hukunci da ilimi. Kamar haka kuwa Muke saka wa masu kyautatawa



Sura: Suratul Qasas

Aya : 15

وَدَخَلَ ٱلۡمَدِينَةَ عَلَىٰ حِينِ غَفۡلَةٖ مِّنۡ أَهۡلِهَا فَوَجَدَ فِيهَا رَجُلَيۡنِ يَقۡتَتِلَانِ هَٰذَا مِن شِيعَتِهِۦ وَهَٰذَا مِنۡ عَدُوِّهِۦۖ فَٱسۡتَغَٰثَهُ ٱلَّذِي مِن شِيعَتِهِۦ عَلَى ٱلَّذِي مِنۡ عَدُوِّهِۦ فَوَكَزَهُۥ مُوسَىٰ فَقَضَىٰ عَلَيۡهِۖ قَالَ هَٰذَا مِنۡ عَمَلِ ٱلشَّيۡطَٰنِۖ إِنَّهُۥ عَدُوّٞ مُّضِلّٞ مُّبِينٞ

Sai ya shiga cikin birnin a lokacin hutawar mutanensa, sai ya sami mutum biyu a cikinsa suna faxa; wannan xan qabilarsa ne, wannan kuma daga maqiyansa, sai xan qabilar tasa ya nemi taimakonsa a kan wanda yake daga maqiyansa; to sai Musa ya naushe shi, sai kuwa ya kashe shi; (da ya ga haka sai) ya ce: “Wannan yana daga aikin Shaixan, lalle shi kuwa maqiyi ne mai vatarwa na fili.”



Sura: Suratul Qasas

Aya : 16

قَالَ رَبِّ إِنِّي ظَلَمۡتُ نَفۡسِي فَٱغۡفِرۡ لِي فَغَفَرَ لَهُۥٓۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلۡغَفُورُ ٱلرَّحِيمُ

Ya ce: “Ya Ubangijina, lalle ni na zalunci kaina, sai Ka yi min gafara,” sai ko Ya yi masa gafara. Lalle Shi kuwa Mai gafara ne, Mai jin qai



Sura: Suratul Qasas

Aya : 17

قَالَ رَبِّ بِمَآ أَنۡعَمۡتَ عَلَيَّ فَلَنۡ أَكُونَ ظَهِيرٗا لِّلۡمُجۡرِمِينَ

Ya ce: “Ya Ubangijina, saboda ni’imar da Ka yi min, ba zan tava zama mai taimakon masu laifi ba.”



Sura: Suratul Qasas

Aya : 18

فَأَصۡبَحَ فِي ٱلۡمَدِينَةِ خَآئِفٗا يَتَرَقَّبُ فَإِذَا ٱلَّذِي ٱسۡتَنصَرَهُۥ بِٱلۡأَمۡسِ يَسۡتَصۡرِخُهُۥۚ قَالَ لَهُۥ مُوسَىٰٓ إِنَّكَ لَغَوِيّٞ مُّبِينٞ

Sai ya wayi gari a cikin birnin a tsorace yana xar-xar, sai ga wanda ya nemi taimakon nan nasa a jiya yana sake neman taimakonsa, (sai) Musa ya ce da shi: “Lalle kai dai vatacce ne a fili!”



Sura: Suratul Qasas

Aya : 19

فَلَمَّآ أَنۡ أَرَادَ أَن يَبۡطِشَ بِٱلَّذِي هُوَ عَدُوّٞ لَّهُمَا قَالَ يَٰمُوسَىٰٓ أَتُرِيدُ أَن تَقۡتُلَنِي كَمَا قَتَلۡتَ نَفۡسَۢا بِٱلۡأَمۡسِۖ إِن تُرِيدُ إِلَّآ أَن تَكُونَ جَبَّارٗا فِي ٱلۡأَرۡضِ وَمَا تُرِيدُ أَن تَكُونَ مِنَ ٱلۡمُصۡلِحِينَ

To lokacin da ya nufi wawurar abokin gabar tasu (sai mai neman taimakon) ya ce: “Ya Musa, shin yanzu nufi kake ka kashe ni kamar yadda ka kashe rai a jiya? Ba abin da kake nufi sai ka zama mai tsaurin rai a bayan qasa; ba ka kuma nufin ka zama cikin masu kawo gyara.”



Sura: Suratul Qasas

Aya : 20

وَجَآءَ رَجُلٞ مِّنۡ أَقۡصَا ٱلۡمَدِينَةِ يَسۡعَىٰ قَالَ يَٰمُوسَىٰٓ إِنَّ ٱلۡمَلَأَ يَأۡتَمِرُونَ بِكَ لِيَقۡتُلُوكَ فَٱخۡرُجۡ إِنِّي لَكَ مِنَ ٱلنَّـٰصِحِينَ

Sai wani mutum (mumini daga mutanen Fir’auna) ya zo daga can qarshen birnin yana gaggawa, ya ce: “Ya Musa, lalle manyan gari (suna can) suna shawara a kanka don su kashe ka, to ka fita (daga birnin nan), lalle ni ina cikin masu yi maka nasiha.”