ٱلَّذِينَ يُؤۡمِنُونَ بِٱلۡغَيۡبِ وَيُقِيمُونَ ٱلصَّلَوٰةَ وَمِمَّا رَزَقۡنَٰهُمۡ يُنفِقُونَ
Waxanda suke yin imani da gaibi kuma suke tsayar da salla kuma suke ciyarwa daga abin da Muka arzuta su da shi
وَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُواْ ٱلزَّكَوٰةَ وَٱرۡكَعُواْ مَعَ ٱلرَّـٰكِعِينَ
Kuma ku tsayar da salla, ku kuma ba da zakka, kuma ku yi ruku’i tare da masu ruku’i
وَٱسۡتَعِينُواْ بِٱلصَّبۡرِ وَٱلصَّلَوٰةِۚ وَإِنَّهَا لَكَبِيرَةٌ إِلَّا عَلَى ٱلۡخَٰشِعِينَ
Kuma ku nemi agaji ta hanyar haquri da kuma salla, kuma lalle ita (salla) babban abu ne sai dai ga masu qasqantar da kai
وَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُواْ ٱلزَّكَوٰةَۚ وَمَا تُقَدِّمُواْ لِأَنفُسِكُم مِّنۡ خَيۡرٖ تَجِدُوهُ عِندَ ٱللَّهِۗ إِنَّ ٱللَّهَ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرٞ
Kuma ku tsayar da salla ku kuma ba da zakka; kuma duk abin da kuka aikata na alheri domin kawunanku za ku same shi a wajen Allah. Lalle Allah Mai ganin abin da kuke aikatawa ne
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱسۡتَعِينُواْ بِٱلصَّبۡرِ وَٱلصَّلَوٰةِۚ إِنَّ ٱللَّهَ مَعَ ٱلصَّـٰبِرِينَ
Ya ku waxanda suka yi imani ku nemi taimako ta hanyar haquri da salla. Lalle Allah Yana tare da masu haquri
حَٰفِظُواْ عَلَى ٱلصَّلَوَٰتِ وَٱلصَّلَوٰةِ ٱلۡوُسۡطَىٰ وَقُومُواْ لِلَّهِ قَٰنِتِينَ
Ku kiyaye salloli da kuma salla mafificiya, kuma ku tsaya domin Allah kuna masu nutsuwa
وَإِذَا ضَرَبۡتُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَلَيۡسَ عَلَيۡكُمۡ جُنَاحٌ أَن تَقۡصُرُواْ مِنَ ٱلصَّلَوٰةِ إِنۡ خِفۡتُمۡ أَن يَفۡتِنَكُمُ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْۚ إِنَّ ٱلۡكَٰفِرِينَ كَانُواْ لَكُمۡ عَدُوّٗا مُّبِينٗا
Kuma idan kun yi tafiya a bayan qasa, to babu laifi a kanku ku yi sallar qasaru[1], in kun ji tsoron kafirai su fitine ku[2]. Lalle kafirai sun kasance maqiya ne, masu bayyana qiyayya a gare ku
1- Watau ku taqaita salloli masu raka’a huxu zuwa raka’a biyu.
2- Ko da yake an ambaci halin tsoron fitinar kafirai, to amma wannan ba sharaxi ba ne, duk wanda yake a halin tafiya yana iya yin sallar qasaru.
وَإِذَا كُنتَ فِيهِمۡ فَأَقَمۡتَ لَهُمُ ٱلصَّلَوٰةَ فَلۡتَقُمۡ طَآئِفَةٞ مِّنۡهُم مَّعَكَ وَلۡيَأۡخُذُوٓاْ أَسۡلِحَتَهُمۡۖ فَإِذَا سَجَدُواْ فَلۡيَكُونُواْ مِن وَرَآئِكُمۡ وَلۡتَأۡتِ طَآئِفَةٌ أُخۡرَىٰ لَمۡ يُصَلُّواْ فَلۡيُصَلُّواْ مَعَكَ وَلۡيَأۡخُذُواْ حِذۡرَهُمۡ وَأَسۡلِحَتَهُمۡۗ وَدَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَوۡ تَغۡفُلُونَ عَنۡ أَسۡلِحَتِكُمۡ وَأَمۡتِعَتِكُمۡ فَيَمِيلُونَ عَلَيۡكُم مَّيۡلَةٗ وَٰحِدَةٗۚ وَلَا جُنَاحَ عَلَيۡكُمۡ إِن كَانَ بِكُمۡ أَذٗى مِّن مَّطَرٍ أَوۡ كُنتُم مَّرۡضَىٰٓ أَن تَضَعُوٓاْ أَسۡلِحَتَكُمۡۖ وَخُذُواْ حِذۡرَكُمۡۗ إِنَّ ٱللَّهَ أَعَدَّ لِلۡكَٰفِرِينَ عَذَابٗا مُّهِينٗا
Kuma idan ka kasance a cikinsu, sai ka yi musu limancin salla[1], to sai wata qungiya su tsaya tare da kai, kuma su riqe makamansu, to yayin da suka yi sujada (wato salla), sai su koma bayanku, sai xaya qungiyar wadda ba su yi salla ba, su zo su yi salla tare da kai, kuma su ma su yi taka-tsantsan, su kuma riqe makamansu. Kafirai kuwa suna burin ina ma za ku gafala ku ajiye makamanku da kayayyakin guzurinku, sai su far muku gaba xaya. Kuma idan akwai wata cuta tare da ku saboda ruwan sama ko kun kasance marasa lafiya, to babu laifi a gare ku ku ajiye makamanku, amma fa ku yi taka-tsantsan. Lalle Allah Ya yi wa kafirai tanadin wata azaba mai wulaqantarwa
1- Watau yadda zai yi wa sahabbansa limancin salla a lokacin da ake cikin halin yaqi.
فَإِذَا قَضَيۡتُمُ ٱلصَّلَوٰةَ فَٱذۡكُرُواْ ٱللَّهَ قِيَٰمٗا وَقُعُودٗا وَعَلَىٰ جُنُوبِكُمۡۚ فَإِذَا ٱطۡمَأۡنَنتُمۡ فَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَۚ إِنَّ ٱلصَّلَوٰةَ كَانَتۡ عَلَى ٱلۡمُؤۡمِنِينَ كِتَٰبٗا مَّوۡقُوتٗا
To idan kun kammala salla, to sai ku ambaci Allah a tsaye ko a zaune ko kuma a kwance. To idan kuka samu nutsuwa sai ku tsayar da salla (a yadda take). Lalle salla ta kasance wata farilla ce mai qayyadajjen lokaci a kan muminai
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا قُمۡتُمۡ إِلَى ٱلصَّلَوٰةِ فَٱغۡسِلُواْ وُجُوهَكُمۡ وَأَيۡدِيَكُمۡ إِلَى ٱلۡمَرَافِقِ وَٱمۡسَحُواْ بِرُءُوسِكُمۡ وَأَرۡجُلَكُمۡ إِلَى ٱلۡكَعۡبَيۡنِۚ وَإِن كُنتُمۡ جُنُبٗا فَٱطَّهَّرُواْۚ وَإِن كُنتُم مَّرۡضَىٰٓ أَوۡ عَلَىٰ سَفَرٍ أَوۡ جَآءَ أَحَدٞ مِّنكُم مِّنَ ٱلۡغَآئِطِ أَوۡ لَٰمَسۡتُمُ ٱلنِّسَآءَ فَلَمۡ تَجِدُواْ مَآءٗ فَتَيَمَّمُواْ صَعِيدٗا طَيِّبٗا فَٱمۡسَحُواْ بِوُجُوهِكُمۡ وَأَيۡدِيكُم مِّنۡهُۚ مَا يُرِيدُ ٱللَّهُ لِيَجۡعَلَ عَلَيۡكُم مِّنۡ حَرَجٖ وَلَٰكِن يُرِيدُ لِيُطَهِّرَكُمۡ وَلِيُتِمَّ نِعۡمَتَهُۥ عَلَيۡكُمۡ لَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ
Ya ku waxanda suka yi imani, idan kun tashi za ku yi salla, to ku wanke fuskokinku da hannayenku zuwa gwiwoyinsu, kuma ku shafi kawunanku, kuma (ku wanke) qafafunku zuwa idon sawu. Kuma idan kun kasance masu janaba, to sai ku tsarkaka. Idan kuma kun kasance marasa lafiya, ko a halin tafiya, ko xaya daga cikinku ya dawo daga bayan gari, ko kuka sadu da mata, kuma sai ba ku sami ruwa ba, to ku yi taimama a doron qasa mai tsarki, ku shafi fuskokinku da hannayenku daga shi. Allah ba Yana nufin Ya sanya qunci a tare da ku ba ne, a’a, Yana nufi ne Ya tsarkake ku, kuma Ya cika ni’imarsa a gare ku, don ku zamo masu godiya
وَأَنۡ أَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَٱتَّقُوهُۚ وَهُوَ ٱلَّذِيٓ إِلَيۡهِ تُحۡشَرُونَ
“Kuma ku tsayar da salla kuma ku kiyaye dokokinsa. Kuma Shi ne Wanda za a tara ku zuwa gare Shi
وَهَٰذَا كِتَٰبٌ أَنزَلۡنَٰهُ مُبَارَكٞ مُّصَدِّقُ ٱلَّذِي بَيۡنَ يَدَيۡهِ وَلِتُنذِرَ أُمَّ ٱلۡقُرَىٰ وَمَنۡ حَوۡلَهَاۚ وَٱلَّذِينَ يُؤۡمِنُونَ بِٱلۡأٓخِرَةِ يُؤۡمِنُونَ بِهِۦۖ وَهُمۡ عَلَىٰ صَلَاتِهِمۡ يُحَافِظُونَ
Kuma wannan (Alqur’ani) littafi ne mai albarka, wanda Muka saukar da shi mai gaskata abin da ya gabace shi (na littattafai), kuma don ka gargaxi uwar alqaryu (mutanen Makka) da waxanda suke kewaye da ita. Waxanda kuwa suke yin imani da ranar lahira, suna yin imani da shi ne (Alqur’ani), kuma su suna kiyaye sallolinsu
وَٱلَّذِينَ يُمَسِّكُونَ بِٱلۡكِتَٰبِ وَأَقَامُواْ ٱلصَّلَوٰةَ إِنَّا لَا نُضِيعُ أَجۡرَ ٱلۡمُصۡلِحِينَ
Waxanda kuwa suke riqo da Littafi, kuma suke tsayar da salla, to lalle Mu ba ma tozarta ladan masu gyara
ٱلَّذِينَ يُقِيمُونَ ٱلصَّلَوٰةَ وَمِمَّا رَزَقۡنَٰهُمۡ يُنفِقُونَ
Waxanda suke tsayar da salla kuma suke ciyarwa daga abin da muka arzurta su
وَمَا كَانَ صَلَاتُهُمۡ عِندَ ٱلۡبَيۡتِ إِلَّا مُكَآءٗ وَتَصۡدِيَةٗۚ فَذُوقُواْ ٱلۡعَذَابَ بِمَا كُنتُمۡ تَكۡفُرُونَ
Kuma sallarsu a Xakin (Ka’aba) ba ta zamanto ba sai fito da tafi. Sai ku xanxani azaba saboda abin da kuka zamanto kuna yi na kafirci
فَإِذَا ٱنسَلَخَ ٱلۡأَشۡهُرُ ٱلۡحُرُمُ فَٱقۡتُلُواْ ٱلۡمُشۡرِكِينَ حَيۡثُ وَجَدتُّمُوهُمۡ وَخُذُوهُمۡ وَٱحۡصُرُوهُمۡ وَٱقۡعُدُواْ لَهُمۡ كُلَّ مَرۡصَدٖۚ فَإِن تَابُواْ وَأَقَامُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتَوُاْ ٱلزَّكَوٰةَ فَخَلُّواْ سَبِيلَهُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ
To idan watanni masu alfarma suka wuce[1] sai ku yaqi mushrikai a duk inda kuka same su, ku kuma kama su ku tsare su ku kuma toshe musu kowace hanya. To amma idan sun tuba sun kuma tsai da salla kuma sun ba da zakka, to sai ku qyale su. Lalle Allah Mai gafara ne Mai jin qai
1- Su ne watanni huxu masu alfarma, watau Zulqi’ida da Zulhijja da Al-Muharram da Rajab.
فَإِن تَابُواْ وَأَقَامُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتَوُاْ ٱلزَّكَوٰةَ فَإِخۡوَٰنُكُمۡ فِي ٱلدِّينِۗ وَنُفَصِّلُ ٱلۡأٓيَٰتِ لِقَوۡمٖ يَعۡلَمُونَ
To idan sun tuba, suka kuma tsayar da salla kuma suka ba da zakka, to sun zama ‘yan’uwanku a cikin addini. Muna kuwa bayanin ayoyi ne filla-filla ga mutane da suke da sani
إِنَّمَا يَعۡمُرُ مَسَٰجِدَ ٱللَّهِ مَنۡ ءَامَنَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ وَأَقَامَ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتَى ٱلزَّكَوٰةَ وَلَمۡ يَخۡشَ إِلَّا ٱللَّهَۖ فَعَسَىٰٓ أُوْلَـٰٓئِكَ أَن يَكُونُواْ مِنَ ٱلۡمُهۡتَدِينَ
Lalle mai raya masallatan Allah shi ne kawai wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira ya kuma tsayar da salla, kuma ya ba da zakka, bai kuma ji tsoron wani ba sai Allah. To waxannan tabbas suna cikin shiryayyu
وَٱلۡمُؤۡمِنُونَ وَٱلۡمُؤۡمِنَٰتُ بَعۡضُهُمۡ أَوۡلِيَآءُ بَعۡضٖۚ يَأۡمُرُونَ بِٱلۡمَعۡرُوفِ وَيَنۡهَوۡنَ عَنِ ٱلۡمُنكَرِ وَيُقِيمُونَ ٱلصَّلَوٰةَ وَيُؤۡتُونَ ٱلزَّكَوٰةَ وَيُطِيعُونَ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥٓۚ أُوْلَـٰٓئِكَ سَيَرۡحَمُهُمُ ٱللَّهُۗ إِنَّ ٱللَّهَ عَزِيزٌ حَكِيمٞ
Muminai maza da muninai mata kuwa masoyan juna ne: Suna yin umurni da kyakkyawan abu suna kuma hana mummunan, suna kuma tsai da salla suna ba da zakka suna kuma bin Allah da Manzonsa. Waxannan Allah zai yi musu rahama. Lalle Allah kuwa Mabuwayi ne Mai hikima
وَأَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰ مُوسَىٰ وَأَخِيهِ أَن تَبَوَّءَا لِقَوۡمِكُمَا بِمِصۡرَ بُيُوتٗا وَٱجۡعَلُواْ بُيُوتَكُمۡ قِبۡلَةٗ وَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَۗ وَبَشِّرِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Kuma Muka yi wa Musa wahayi shi da xan’uwansa cewa: “Ku tanadar wa mutanenku gidaje a Masar, ku kuma sanya gidajenku wurin salla.” Ka kuma yi wa muminai albishir (da samun nasara)
وَأَقِمِ ٱلصَّلَوٰةَ طَرَفَيِ ٱلنَّهَارِ وَزُلَفٗا مِّنَ ٱلَّيۡلِۚ إِنَّ ٱلۡحَسَنَٰتِ يُذۡهِبۡنَ ٱلسَّيِّـَٔاتِۚ ذَٰلِكَ ذِكۡرَىٰ لِلذَّـٰكِرِينَ
Ka kuma tsai da salla farkon rana da qarshenta da kuma farkon dare. Lalle kyawawan (ayyuka) suna shafe munana. Wannan tunasarwa ne ga masu tunawa
وَٱلَّذِينَ صَبَرُواْ ٱبۡتِغَآءَ وَجۡهِ رَبِّهِمۡ وَأَقَامُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَأَنفَقُواْ مِمَّا رَزَقۡنَٰهُمۡ سِرّٗا وَعَلَانِيَةٗ وَيَدۡرَءُونَ بِٱلۡحَسَنَةِ ٱلسَّيِّئَةَ أُوْلَـٰٓئِكَ لَهُمۡ عُقۡبَى ٱلدَّارِ
Waxanda kuma suka yi haquri don neman yardar Ubangijnsu, suka kuma tsai da salla, kuma suka ciyar daga abin da Muka arzuta su da shi a voye da sarari, suke kuma ingije mummunan aiki da kyakkyawa, waxannan suna da (kyakkyawar) makoma ta gidan (Aljanna)
قُل لِّعِبَادِيَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ يُقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَيُنفِقُواْ مِمَّا رَزَقۡنَٰهُمۡ سِرّٗا وَعَلَانِيَةٗ مِّن قَبۡلِ أَن يَأۡتِيَ يَوۡمٞ لَّا بَيۡعٞ فِيهِ وَلَا خِلَٰلٌ
Ka ce da bayina waxanda suka yi imani, su tsayar da salla kuma su ciyar daga abin da Muka arzuta su da shi, a voye da sarari tun kafin zuwan ranar da babu ciniki a cikinta, kuma babu abota
رَّبَّنَآ إِنِّيٓ أَسۡكَنتُ مِن ذُرِّيَّتِي بِوَادٍ غَيۡرِ ذِي زَرۡعٍ عِندَ بَيۡتِكَ ٱلۡمُحَرَّمِ رَبَّنَا لِيُقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ فَٱجۡعَلۡ أَفۡـِٔدَةٗ مِّنَ ٱلنَّاسِ تَهۡوِيٓ إِلَيۡهِمۡ وَٱرۡزُقۡهُم مِّنَ ٱلثَّمَرَٰتِ لَعَلَّهُمۡ يَشۡكُرُونَ
“Ya Ubangijinmu, lalle ni na zaunar da wasu daga zuriyata a wani kwari wanda ba a shuka a cikinsa[1] kusa da Xakinka mai alfarma; ya Ubangijinmu don su tsai da salla, to Ka sanya zukatan mutane su riqa karkatowa zuwa gare su, kuma Ka arzuta su da ‘ya’yan itace don su gode (maka)
1- Watau kuyangarsa Hajara () da xansa Isma’ilu (). Ya zaunar da su garin Makka da izinin Allah ().
رَبِّ ٱجۡعَلۡنِي مُقِيمَ ٱلصَّلَوٰةِ وَمِن ذُرِّيَّتِيۚ رَبَّنَا وَتَقَبَّلۡ دُعَآءِ
“Ya Ubangijina, Ka sanya ni in zama mai tsayar da salla da kuma zuriyata. Ya Ubangijinmu, Ka karvi addu’ata
أَقِمِ ٱلصَّلَوٰةَ لِدُلُوكِ ٱلشَّمۡسِ إِلَىٰ غَسَقِ ٱلَّيۡلِ وَقُرۡءَانَ ٱلۡفَجۡرِۖ إِنَّ قُرۡءَانَ ٱلۡفَجۡرِ كَانَ مَشۡهُودٗا
Ka tsayar da salla lokacin zawalin rana zuwa duhun dare[1], da kuma karatun sallar Asuba. Lalle (lokacin) karatun sallar asuba ya kasance lokacin halartar (mala’iku)
1- Wannan lokaci ya qunshi sallar azahar da la’asar da magriba da isha’i.
قُلِ ٱدۡعُواْ ٱللَّهَ أَوِ ٱدۡعُواْ ٱلرَّحۡمَٰنَۖ أَيّٗا مَّا تَدۡعُواْ فَلَهُ ٱلۡأَسۡمَآءُ ٱلۡحُسۡنَىٰۚ وَلَا تَجۡهَرۡ بِصَلَاتِكَ وَلَا تُخَافِتۡ بِهَا وَٱبۡتَغِ بَيۡنَ ذَٰلِكَ سَبِيلٗا
Ka ce: “Ku kira (sunan) Allah ko ku kira (sunan) Arrahaman; kowanne kuka kira to shi Yana da sunaye ne mafiya kyau.” Kada kuma ka xaga muryarka da (karatun) sallarka, kada kuma ka yi shi a voye, ka nemi tsaka-tsakin wannan
وَجَعَلَنِي مُبَارَكًا أَيۡنَ مَا كُنتُ وَأَوۡصَٰنِي بِٱلصَّلَوٰةِ وَٱلزَّكَوٰةِ مَا دُمۡتُ حَيّٗا
“Ya kuma sanya ni mai albarka a duk inda nake, kuma Ya umarce ni da yin salla da kuma ba da zakka matuqar ina raye
وَكَانَ يَأۡمُرُ أَهۡلَهُۥ بِٱلصَّلَوٰةِ وَٱلزَّكَوٰةِ وَكَانَ عِندَ رَبِّهِۦ مَرۡضِيّٗا
Kuma ya zamanto yana umartar iyalinsa da (tsai da) salla da kuma (ba da) zakka, kuma shi yardajje ne a wurin Ubangijinsa
۞فَخَلَفَ مِنۢ بَعۡدِهِمۡ خَلۡفٌ أَضَاعُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَٱتَّبَعُواْ ٱلشَّهَوَٰتِۖ فَسَوۡفَ يَلۡقَوۡنَ غَيًّا
Sai wasu suka maye gurbinsu bayansu waxanda suka tozarta salla suka kuma bi sha’awace-sha’awacen (duniya na savo); to ba da daxewa ba za su haxu da mummunan sharri (a Jahannama)