Sura: Suratul Anbiya

Aya : 10

لَقَدۡ أَنزَلۡنَآ إِلَيۡكُمۡ كِتَٰبٗا فِيهِ ذِكۡرُكُمۡۚ أَفَلَا تَعۡقِلُونَ

Haqiqa Mun saukar muku da littafi (wanda) a cikinsa akwai xaukakarku[1]; me ya sa ba kwa hankalta?


1- Watau za su samu xaukaka duniya da lahira idan sun yi imani da shi, suka yi aiki da karantarwarsa.


Sura: Suratul Anbiya

Aya : 50

وَهَٰذَا ذِكۡرٞ مُّبَارَكٌ أَنزَلۡنَٰهُۚ أَفَأَنتُمۡ لَهُۥ مُنكِرُونَ

Wannan (Alqur’ani) kuwa tunatarwa ne mai albarka da Muka saukar da shi. Shin ku yanzu kwa riqa musun sa?



Sura: Suratul Hajji

Aya : 16

وَكَذَٰلِكَ أَنزَلۡنَٰهُ ءَايَٰتِۭ بَيِّنَٰتٖ وَأَنَّ ٱللَّهَ يَهۡدِي مَن يُرِيدُ

Kamar haka kuwa Muka saukar da shi (Alqur’ani) ayoyi mabayyana, kuma lalle Allah Yana shiryar da wanda Yake nufin (shiryar da shi)



Sura: Suratun Nur

Aya : 34

وَلَقَدۡ أَنزَلۡنَآ إِلَيۡكُمۡ ءَايَٰتٖ مُّبَيِّنَٰتٖ وَمَثَلٗا مِّنَ ٱلَّذِينَ خَلَوۡاْ مِن قَبۡلِكُمۡ وَمَوۡعِظَةٗ لِّلۡمُتَّقِينَ

Haqiqa kuma Mun saukar muku da ayoyi mabayyana da kuma izina daga waxanda suka wuce gabaninku, kuma da gargaxi ga masu taqawa



Sura: Suratun Nur

Aya : 46

لَّقَدۡ أَنزَلۡنَآ ءَايَٰتٖ مُّبَيِّنَٰتٖۚ وَٱللَّهُ يَهۡدِي مَن يَشَآءُ إِلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ

Haqiqa Mun saukar da ayoyi masu bayyana komai da komai. Allah kuma Yana shiryar da wanda Ya ga dama zuwa ga tafarki madaidaici



Sura: Suratul Furqan

Aya : 6

قُلۡ أَنزَلَهُ ٱلَّذِي يَعۡلَمُ ٱلسِّرَّ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ إِنَّهُۥ كَانَ غَفُورٗا رَّحِيمٗا

Ka ce (da su): “Wanda Yake sane da asirin sammai da qasa Shi Ya saukar da shi. Lalle Shi Ya kasance Mai gafara ne, Mai jin qai.”



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 192

وَإِنَّهُۥ لَتَنزِيلُ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Kuma lalle shi (Alqur’ani) saukarwa ce ta Ubangijin talikai



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 193

نَزَلَ بِهِ ٱلرُّوحُ ٱلۡأَمِينُ

Ruhi amintacce (watau Jibrilu) ne ya sauko da shi



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 194

عَلَىٰ قَلۡبِكَ لِتَكُونَ مِنَ ٱلۡمُنذِرِينَ

A bisa zuciyarka don ka zamanto daga masu gargaxi



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 195

بِلِسَانٍ عَرَبِيّٖ مُّبِينٖ

(Ya saukar da shi) da harshen Larabci mabayyani



Sura: Suratul Qasas

Aya : 86

وَمَا كُنتَ تَرۡجُوٓاْ أَن يُلۡقَىٰٓ إِلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبُ إِلَّا رَحۡمَةٗ مِّن رَّبِّكَۖ فَلَا تَكُونَنَّ ظَهِيرٗا لِّلۡكَٰفِرِينَ

Kuma ba ka kasance kana fatan a saukar maka da littafi ba, sai dai (an yi haka ne) don rahama daga Ubangijinka; to don haka kada ka zamanto mai taimakon kafirai



Sura: Suratul Ankabut

Aya : 51

أَوَلَمۡ يَكۡفِهِمۡ أَنَّآ أَنزَلۡنَا عَلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ يُتۡلَىٰ عَلَيۡهِمۡۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَرَحۡمَةٗ وَذِكۡرَىٰ لِقَوۡمٖ يُؤۡمِنُونَ

Yanzu bai ishe su ba cewa, Mun saukar maka da Littafi da ake karanta musu shi? Lalle a game da wannan tabbas akwai rahama da kuma tunatarwa ga mutanen da suke yin imani



Sura: Suratus Sajda

Aya : 2

تَنزِيلُ ٱلۡكِتَٰبِ لَا رَيۡبَ فِيهِ مِن رَّبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Saukar da Littafin da babu kokwanto a cikinsa daga Ubangijin talikai ne



Sura: Suratu Faxir

Aya : 31

وَٱلَّذِيٓ أَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡكَ مِنَ ٱلۡكِتَٰبِ هُوَ ٱلۡحَقُّ مُصَدِّقٗا لِّمَا بَيۡنَ يَدَيۡهِۗ إِنَّ ٱللَّهَ بِعِبَادِهِۦ لَخَبِيرُۢ بَصِيرٞ

Kuma abin da Muka yiwo maka wahayinsa na Littafi shi ne gaskiya, yana gaskata abin da yake gabaninsa (na littattafai). Lalle Allah game da bayinsa Masani ne, Mai gani



Sura: Suratu Yasin

Aya : 5

تَنزِيلَ ٱلۡعَزِيزِ ٱلرَّحِيمِ

(Alqur’ani) saukarwar (Allah) Mabuwayi Mai jin qai ne



Sura: Suratu Sad

Aya : 29

كِتَٰبٌ أَنزَلۡنَٰهُ إِلَيۡكَ مُبَٰرَكٞ لِّيَدَّبَّرُوٓاْ ءَايَٰتِهِۦ وَلِيَتَذَكَّرَ أُوْلُواْ ٱلۡأَلۡبَٰبِ

Littafi ne mai albarka da Muka saukar maka da shi domin su yi tuntuntuni game da ayoyinsa, don kuma masu hankula su wa’azantu



Sura: Suratuz Zumar

Aya : 1

تَنزِيلُ ٱلۡكِتَٰبِ مِنَ ٱللَّهِ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡحَكِيمِ

Saukar Littafi daga Allah ne Mabuwayi, Mai hikima



Sura: Suratuz Zumar

Aya : 2

إِنَّآ أَنزَلۡنَآ إِلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ بِٱلۡحَقِّ فَٱعۡبُدِ ٱللَّهَ مُخۡلِصٗا لَّهُ ٱلدِّينَ

Lalle Mu Muka saukar maka Littafi da gaskiya, to ka bauta wa Allah kana mai tsantsanta addini a gare Shi



Sura: Suratuz Zumar

Aya : 23

ٱللَّهُ نَزَّلَ أَحۡسَنَ ٱلۡحَدِيثِ كِتَٰبٗا مُّتَشَٰبِهٗا مَّثَانِيَ تَقۡشَعِرُّ مِنۡهُ جُلُودُ ٱلَّذِينَ يَخۡشَوۡنَ رَبَّهُمۡ ثُمَّ تَلِينُ جُلُودُهُمۡ وَقُلُوبُهُمۡ إِلَىٰ ذِكۡرِ ٱللَّهِۚ ذَٰلِكَ هُدَى ٱللَّهِ يَهۡدِي بِهِۦ مَن يَشَآءُۚ وَمَن يُضۡلِلِ ٱللَّهُ فَمَا لَهُۥ مِنۡ هَادٍ

Allah Ya saukar da mafi kyan zance: Alqur’ani mai kama da juna, mai biyunta (saqo), tsikar fatun waxanda suke tsoron Ubangijinsu suna tashi, sannan fatunsu su yi taushi, zukatansu kuwa su koma zuwa ambaton Allah. Wannan ita ce shiriyar Allah, Yana shiyar da wanda Ya ga dama da ita. Wanda kuma Allah Ya vatar to ba shi da mai shiryar da shi



Sura: Suratuz Zumar

Aya : 41

إِنَّآ أَنزَلۡنَا عَلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ لِلنَّاسِ بِٱلۡحَقِّۖ فَمَنِ ٱهۡتَدَىٰ فَلِنَفۡسِهِۦۖ وَمَن ضَلَّ فَإِنَّمَا يَضِلُّ عَلَيۡهَاۖ وَمَآ أَنتَ عَلَيۡهِم بِوَكِيلٍ

Lalle Mu Mun saukar maka da Littafi da gaskiya ga mutane; saboda haka duk wanda ya shiriya to ya yi wa kansa alheri, wanda kuwa ya vata, to lalle ya vata ne don kansa; kuma kai ba wakili ba ne a kansu



Sura: Suratu Ghafir

Aya : 2

تَنزِيلُ ٱلۡكِتَٰبِ مِنَ ٱللَّهِ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡعَلِيمِ

Saukarwar Littafi daga Allah ne Mabuwayi, Masani



Sura: Suratu Fussilat

Aya : 2

تَنزِيلٞ مِّنَ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

(Alqur’ani) saukakke ne daga (Allah) Mai rahama, Mai jin qai



Sura: Suratu Fussilat

Aya : 3

كِتَٰبٞ فُصِّلَتۡ ءَايَٰتُهُۥ قُرۡءَانًا عَرَبِيّٗا لِّقَوۡمٖ يَعۡلَمُونَ

(Shi) Littafi ne Alqur’ani Balarabe da aka rarrabe ayoyinsa ga mutanen da suke sanin (ma’anarsa)



Sura: Suratu Fussilat

Aya : 4

بَشِيرٗا وَنَذِيرٗا فَأَعۡرَضَ أَكۡثَرُهُمۡ فَهُمۡ لَا يَسۡمَعُونَ

Mai albishir ne kuma mai gargaxi, sai yawancinsu suka bijire, don haka su ba sa jin (kira)



Sura: Suratu Fussilat

Aya : 41

إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِٱلذِّكۡرِ لَمَّا جَآءَهُمۡۖ وَإِنَّهُۥ لَكِتَٰبٌ عَزِيزٞ

Lalle waxanda suka kafirce wa Alqur’ani lokacin da ya zo musu (tabbas Allah zai saka musu). Lalle kuma shi littafi ne mabuwayi



Sura: Suratu Fussilat

Aya : 42

لَّا يَأۡتِيهِ ٱلۡبَٰطِلُ مِنۢ بَيۡنِ يَدَيۡهِ وَلَا مِنۡ خَلۡفِهِۦۖ تَنزِيلٞ مِّنۡ حَكِيمٍ حَمِيدٖ

Varna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa; saukakke ne daga Mai hikima, Sha-yabo



Sura: Suratus Shura

Aya : 17

ٱللَّهُ ٱلَّذِيٓ أَنزَلَ ٱلۡكِتَٰبَ بِٱلۡحَقِّ وَٱلۡمِيزَانَۗ وَمَا يُدۡرِيكَ لَعَلَّ ٱلسَّاعَةَ قَرِيبٞ

Allah ne Ya saukar da Littafi da gaskiya da kuma adalci. Me yake sanar da kai cewa ko alqiyama kusa take



Sura: Suratus Shura

Aya : 52

وَكَذَٰلِكَ أَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡكَ رُوحٗا مِّنۡ أَمۡرِنَاۚ مَا كُنتَ تَدۡرِي مَا ٱلۡكِتَٰبُ وَلَا ٱلۡإِيمَٰنُ وَلَٰكِن جَعَلۡنَٰهُ نُورٗا نَّهۡدِي بِهِۦ مَن نَّشَآءُ مِنۡ عِبَادِنَاۚ وَإِنَّكَ لَتَهۡدِيٓ إِلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ

Kuma kamar haka ne Muka yiwo maka wahayin Ruhi (watau Alqur’ani) daga umarninmu. Ba ka zamanto ka san mene ne littafi ko kuma imani ba, sai dai kuma Mun sanya shi (Alqur’ani) haske ne da Muke shiryar da wanda Muka ga dama daga bayinmu da shi. Lalle kuma kai tabbas kana shiryarwa zuwa ga tafarki madaidaici



Sura: Suratuz Zukhruf 

Aya : 1

حمٓ

HA MIM[1]


1- Duba Suratul Baqara, aya ta 1, hashiya ta 8.


Sura: Suratuz Zukhruf 

Aya : 2

وَٱلۡكِتَٰبِ ٱلۡمُبِينِ

Na rantse da Littafi mabayyani (Alqur’ani)