Sura: Suratuz Zukhruf 

Aya : 3

إِنَّا جَعَلۡنَٰهُ قُرۡءَٰنًا عَرَبِيّٗا لَّعَلَّكُمۡ تَعۡقِلُونَ

Lalle Mu Mun sanya shi ya zamo abin karantawa cikin harshen Larabci domin ku hankalta



Sura: Suratuz Zukhruf 

Aya : 4

وَإِنَّهُۥ فِيٓ أُمِّ ٱلۡكِتَٰبِ لَدَيۡنَا لَعَلِيٌّ حَكِيمٌ

Lalle kuma shi (Alqur’ani) a cikin Littafi Lauhul-Mahafuzu a wurinmu tabbas maxaukaki ne, mai hikima



Sura: Suratud Dukhan

Aya : 2

وَٱلۡكِتَٰبِ ٱلۡمُبِينِ

Na rantse da Littafi mai bayyanawa (shi ne Alqur’ani)



Sura: Suratud Dukhan

Aya : 3

إِنَّآ أَنزَلۡنَٰهُ فِي لَيۡلَةٖ مُّبَٰرَكَةٍۚ إِنَّا كُنَّا مُنذِرِينَ

Lalle Mu Muka saukar da shi a cikin dare mai albarka[1]. Lalle Mu Mun kasance Masu gargaxi


1- Shi ne daren Lailatul Qadari. Duba Suratul Qadri.


Sura: Suratul Jasiya

Aya : 2

تَنزِيلُ ٱلۡكِتَٰبِ مِنَ ٱللَّهِ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡحَكِيمِ

Saukar da Alqur’ani daga Allah ne Mabuwayi, Mai hikima



Sura: Suratul Jasiya

Aya : 6

تِلۡكَ ءَايَٰتُ ٱللَّهِ نَتۡلُوهَا عَلَيۡكَ بِٱلۡحَقِّۖ فَبِأَيِّ حَدِيثِۭ بَعۡدَ ٱللَّهِ وَءَايَٰتِهِۦ يُؤۡمِنُونَ

Waxannan su ne ayoyin Allah da Muke karanta maka su da gaskiya; to da wane zance ne za su yi imani bayan (zancen) Allah da ayoyinsa?



Sura: Suratul Ahqaf 

Aya : 2

تَنزِيلُ ٱلۡكِتَٰبِ مِنَ ٱللَّهِ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡحَكِيمِ

Saukar da Alqur’ani daga Allah ne Mabuwayi, Mai hikima



Sura: Suratul Waqi’a

Aya : 77

إِنَّهُۥ لَقُرۡءَانٞ كَرِيمٞ

Lalle shi Alqur’ani ne mai girma



Sura: Suratul Waqi’a

Aya : 78

فِي كِتَٰبٖ مَّكۡنُونٖ

A cikin littafi abin kiyayewa (daga wani sauyi).[1]


1- Shi ne Lauhul Mahfuz.


Sura: Suratul Waqi’a

Aya : 79

لَّا يَمَسُّهُۥٓ إِلَّا ٱلۡمُطَهَّرُونَ

Babu mai tava shi sai tsarkakakku



Sura: Suratul Waqi’a

Aya : 80

تَنزِيلٞ مِّن رَّبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Saukakke ne daga Ubangijin talikai



Sura: Suratul Hadid

Aya : 9

هُوَ ٱلَّذِي يُنَزِّلُ عَلَىٰ عَبۡدِهِۦٓ ءَايَٰتِۭ بَيِّنَٰتٖ لِّيُخۡرِجَكُم مِّنَ ٱلظُّلُمَٰتِ إِلَى ٱلنُّورِۚ وَإِنَّ ٱللَّهَ بِكُمۡ لَرَءُوفٞ رَّحِيمٞ

Shi ne Wanda Yake saukar da ayoyi bayyanannu ga Bawansa don Ya fitar da ku daga duffai zuwa haske. Kuma lalle Allah Mai tausayi ne, Mai rahama a gare ku



Sura: Suratul Haqqa

Aya : 43

تَنزِيلٞ مِّن رَّبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Shi saukakke ne daga Ubangijin halittu



Sura: Suratul Insan

Aya : 23

إِنَّا نَحۡنُ نَزَّلۡنَا عَلَيۡكَ ٱلۡقُرۡءَانَ تَنزِيلٗا

Lalle Mu Muka saukar maka da Alqur’ani daki-daki