Sura: Suratuz Zumar

Aya : 75

وَتَرَى ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةَ حَآفِّينَ مِنۡ حَوۡلِ ٱلۡعَرۡشِ يُسَبِّحُونَ بِحَمۡدِ رَبِّهِمۡۚ وَقُضِيَ بَيۡنَهُم بِٱلۡحَقِّۚ وَقِيلَ ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Kuma za ka ga mala’iku suna kewaye da Al’arshi, suna tasbihi da yabon Ubangijnsu; aka kuma yi hukunci a tsakaninsu (halittu) da gaskiya, aka kuma ce: “Yabo ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai.”



Sura: Suratu Ghafir

Aya : 15

رَفِيعُ ٱلدَّرَجَٰتِ ذُو ٱلۡعَرۡشِ يُلۡقِي ٱلرُّوحَ مِنۡ أَمۡرِهِۦ عَلَىٰ مَن يَشَآءُ مِنۡ عِبَادِهِۦ لِيُنذِرَ يَوۡمَ ٱلتَّلَاقِ

(Shi ne) Mai maxaukakan darajoji, Ma’abocin Al’arshi, Yana sauko da wahayi daga umarninsa ga wanda Ya ga dama daga bayinsa don Ya yi gargaxin ranar haxuwa



Sura: Suratu Ghafir

Aya : 16

يَوۡمَ هُم بَٰرِزُونَۖ لَا يَخۡفَىٰ عَلَى ٱللَّهِ مِنۡهُمۡ شَيۡءٞۚ لِّمَنِ ٱلۡمُلۡكُ ٱلۡيَوۡمَۖ لِلَّهِ ٱلۡوَٰحِدِ ٱلۡقَهَّارِ

Ranar da za su bayyana; babu wani abu nasu da zai vuya ga Allah. (Zai ce): “Mulki na wane ne a yau?” (Sai Ya ce): “Na Allah Makaxaici, Mai rinjaye ne.”



Sura: Suratu Ghafir

Aya : 17

ٱلۡيَوۡمَ تُجۡزَىٰ كُلُّ نَفۡسِۭ بِمَا كَسَبَتۡۚ لَا ظُلۡمَ ٱلۡيَوۡمَۚ إِنَّ ٱللَّهَ سَرِيعُ ٱلۡحِسَابِ

A wannan ranar za a saka wa kowane rai da irin abin da ya aikata. Babu zalunci a wannan ranar. Lalle Allah Mai gaggawar yin hisabi ne



Sura: Suratu Ghafir

Aya : 18

وَأَنذِرۡهُمۡ يَوۡمَ ٱلۡأٓزِفَةِ إِذِ ٱلۡقُلُوبُ لَدَى ٱلۡحَنَاجِرِ كَٰظِمِينَۚ مَا لِلظَّـٰلِمِينَ مِنۡ حَمِيمٖ وَلَا شَفِيعٖ يُطَاعُ

Ka kuma tsoratar da su ranar (alqiyama) mai kusantowa, a yayin da zukata suke maqare a wuyoyinsu (saboda tsananin tsoro). Azzalumai ba su da wani masoyi ko kuma wani mai ceto da za a yi wa biyayya



Sura: Suratus Shura

Aya : 47

ٱسۡتَجِيبُواْ لِرَبِّكُم مِّن قَبۡلِ أَن يَأۡتِيَ يَوۡمٞ لَّا مَرَدَّ لَهُۥ مِنَ ٱللَّهِۚ مَا لَكُم مِّن مَّلۡجَإٖ يَوۡمَئِذٖ وَمَا لَكُم مِّن نَّكِيرٖ

Ku amsa kiran Ubangijinku tun kafin ranar da ba ta da wata makauta[1] ta zo daga Allah. Ba ku da wata mafaka a wannan ranar, kuma ba ku da damar yin musu[2]


1- Watau babu wanda ya isa ya hana zuwanta.


2- Watau ba su da damar musunta zunuban da suka aikata a duniya.


Sura: Suratud Dukhan

Aya : 40

إِنَّ يَوۡمَ ٱلۡفَصۡلِ مِيقَٰتُهُمۡ أَجۡمَعِينَ

Lalle ranar alqiyama ne lokacin da aka qayyade musu gaba xaya



Sura: Suratud Dukhan

Aya : 41

يَوۡمَ لَا يُغۡنِي مَوۡلًى عَن مَّوۡلٗى شَيۡـٔٗا وَلَا هُمۡ يُنصَرُونَ

Ranar da wani masoyi ba zai amfana wa masoyinsa komai ba, su kuma ba za a taimaka musu ba



Sura: Suratud Dukhan

Aya : 42

إِلَّا مَن رَّحِمَ ٱللَّهُۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ

Sai fa wanda Allah Ya ji qan sa. Lalle Shi ne Mabuwayi, Mai rahama



Sura: Suratul Jasiya

Aya : 26

قُلِ ٱللَّهُ يُحۡيِيكُمۡ ثُمَّ يُمِيتُكُمۡ ثُمَّ يَجۡمَعُكُمۡ إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ لَا رَيۡبَ فِيهِ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعۡلَمُونَ

Ka ce: “Allah ne zai raya ku sannan ya kashe ku sannan ya tara ku a ranar alqiyama wadda babu kokwanto game da ita, sai dai kuma yawancin mutane ba sa sanin (haka).”



Sura: Suratu Qaf 

Aya : 20

وَنُفِخَ فِي ٱلصُّورِۚ ذَٰلِكَ يَوۡمُ ٱلۡوَعِيدِ

Aka kuma yi busa a qaho[1]. Wannan ita ce ranar narko


1- Watau busa ta biyu.


Sura: Suratu Qaf 

Aya : 21

وَجَآءَتۡ كُلُّ نَفۡسٖ مَّعَهَا سَآئِقٞ وَشَهِيدٞ

Kuma kowane rai ya zo a tare da shi akwai mai kora da mai shaida[1]


1- Watau mala’iku biyu tare da kowane mutum, xaya yana kora shi; xaya kuma mai ba da shaida game da shi.


Sura: Suratu Qaf 

Aya : 22

لَّقَدۡ كُنتَ فِي غَفۡلَةٖ مِّنۡ هَٰذَا فَكَشَفۡنَا عَنكَ غِطَآءَكَ فَبَصَرُكَ ٱلۡيَوۡمَ حَدِيدٞ

Haqiqa ka kasance a cikin gafala game da wannan, sai Muka yaye maka yanarka, to ganinka a yau tangaran yake



Sura: Suratu Qaf 

Aya : 23

وَقَالَ قَرِينُهُۥ هَٰذَا مَا لَدَيَّ عَتِيدٌ

Mala’ikan da yake tare da shi kuma ya ce: “Wannan shi ne abin da yake hallare a tare da ni.”



Sura: Suratu Qaf 

Aya : 30

يَوۡمَ نَقُولُ لِجَهَنَّمَ هَلِ ٱمۡتَلَأۡتِ وَتَقُولُ هَلۡ مِن مَّزِيدٖ

A ranar da za Mu ce da Jahannama: “Shin kin cika?” (Ita) kuma ta ce: “Shin akwai wani qari?”



Sura: Suratu Qaf 

Aya : 31

وَأُزۡلِفَتِ ٱلۡجَنَّةُ لِلۡمُتَّقِينَ غَيۡرَ بَعِيدٍ

Aka kuma kusantar da Aljanna ga masu tsoron Allah, ba tare da nisa ba



Sura: Suratu Qaf 

Aya : 32

هَٰذَا مَا تُوعَدُونَ لِكُلِّ أَوَّابٍ حَفِيظٖ

(Sai a ce da su): “Wannan ne abin da ake yi muku alqawarinsa, (ga shi nan a tanade) ga duk wani mai yawan komawa ga Allah, mai kiyaye (dokokinsa)



Sura: Suratu Qaf 

Aya : 33

مَّنۡ خَشِيَ ٱلرَّحۡمَٰنَ بِٱلۡغَيۡبِ وَجَآءَ بِقَلۡبٖ مُّنِيبٍ

“Wanda ya ji tsoron Allah a voye, ya zo kuma da zuciya mai komawa ga Allah.”



Sura: Suratu Qaf 

Aya : 34

ٱدۡخُلُوهَا بِسَلَٰمٖۖ ذَٰلِكَ يَوۡمُ ٱلۡخُلُودِ

(Za a ce da su): Ku shige ta da aminci; wannan ita ce ranar dawwama



Sura: Suratu Qaf 

Aya : 35

لَهُم مَّا يَشَآءُونَ فِيهَا وَلَدَيۡنَا مَزِيدٞ

Suna da duk abin da suka dama a cikinta, kuma wurinmu akwai wani qari[1]


1- Watau qarin wasu ni’imomi, daga cikinsu akwai ganin Fuskar Allah da samun yardarsa ta har abada.


Sura: Suratu Qaf 

Aya : 41

وَٱسۡتَمِعۡ يَوۡمَ يُنَادِ ٱلۡمُنَادِ مِن مَّكَانٖ قَرِيبٖ

Ka kuma saurara ranar da mai kira zai yi kira[1] daga wani wuri makusanci


1- Watau mala’ikan da aka wakilta domin busa qaho.


Sura: Suratu Qaf 

Aya : 42

يَوۡمَ يَسۡمَعُونَ ٱلصَّيۡحَةَ بِٱلۡحَقِّۚ ذَٰلِكَ يَوۡمُ ٱلۡخُرُوجِ

A ranar da (talikai) za su ji tsawa ta gaskiya[1]. Wannan ita ce ranar fitowa (daga qabari)


1- Watau busa ta biyu.


Sura: Suratu Qaf 

Aya : 43

إِنَّا نَحۡنُ نُحۡيِۦ وَنُمِيتُ وَإِلَيۡنَا ٱلۡمَصِيرُ

Lalle Mu ne Muke rayawa, Muke kuma kashewa, kuma makoma zuwa gare Mu ne



Sura: Suratu Qaf 

Aya : 44

يَوۡمَ تَشَقَّقُ ٱلۡأَرۡضُ عَنۡهُمۡ سِرَاعٗاۚ ذَٰلِكَ حَشۡرٌ عَلَيۡنَا يَسِيرٞ

A ranar da qasa za ta tsattsage musu (su fito) da gaggawa. Wannan tattarawa ce mai sauqi a gare Mu



Sura: Suratul Hadid

Aya : 12

يَوۡمَ تَرَى ٱلۡمُؤۡمِنِينَ وَٱلۡمُؤۡمِنَٰتِ يَسۡعَىٰ نُورُهُم بَيۡنَ أَيۡدِيهِمۡ وَبِأَيۡمَٰنِهِمۖ بُشۡرَىٰكُمُ ٱلۡيَوۡمَ جَنَّـٰتٞ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَاۚ ذَٰلِكَ هُوَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡعَظِيمُ

(Ka tuna) ranar da za ka ga muminai maza da muminai mata haskensu yana tafiya ta gabansu da ta damansu, (ana cewa da su): “Albishirinku a wannan rana (su ne) gidajen Aljanna da qoramu suke gudana ta qarqashinsu, kuna masu dawwama a cikinsu. Wannan shi ne rabo mai girma.”



Sura: Suratul Hadid

Aya : 13

يَوۡمَ يَقُولُ ٱلۡمُنَٰفِقُونَ وَٱلۡمُنَٰفِقَٰتُ لِلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱنظُرُونَا نَقۡتَبِسۡ مِن نُّورِكُمۡ قِيلَ ٱرۡجِعُواْ وَرَآءَكُمۡ فَٱلۡتَمِسُواْ نُورٗاۖ فَضُرِبَ بَيۡنَهُم بِسُورٖ لَّهُۥ بَابُۢ بَاطِنُهُۥ فِيهِ ٱلرَّحۡمَةُ وَظَٰهِرُهُۥ مِن قِبَلِهِ ٱلۡعَذَابُ

A ranar da munafukai maza da munafukai mata za su riqa cewa da waxanda suka yi imani: “Ku saurara mana mu xan xosani haskenku.” Aka ce (da su): “Ku koma bayanku (watau duniya) sai ku nemi haske.” sai aka raba tsakaninsu da katanga wadda take da wata qofa, daga cikinta akwai rahama, bayanta kuma azaba ce (take bugowa) daga gare ta



Sura: Suratul Qalam

Aya : 42

يَوۡمَ يُكۡشَفُ عَن سَاقٖ وَيُدۡعَوۡنَ إِلَى ٱلسُّجُودِ فَلَا يَسۡتَطِيعُونَ

(Ka tuna) ranar da za a yaye qwauri[1] a kuma kirawo su zuwa yin sujjada sannan su rasa ikon yi


1- Watau ranar da Allah () zai kware qwaurinsa mai daraja wanda bai yi kama da wani abu na halittarsa ba.


Sura: Suratul Qalam

Aya : 43

خَٰشِعَةً أَبۡصَٰرُهُمۡ تَرۡهَقُهُمۡ ذِلَّةٞۖ وَقَدۡ كَانُواْ يُدۡعَوۡنَ إِلَى ٱلسُّجُودِ وَهُمۡ سَٰلِمُونَ

Idanuwansu a qasqance, wulaqanci ya lulluve su. Haqiqa kuwa a duniya sun kasance ana kiran su zuwa yin sujjada alhali suna lafiyayyu



Sura: Suratul Haqqa

Aya : 13

فَإِذَا نُفِخَ فِي ٱلصُّورِ نَفۡخَةٞ وَٰحِدَةٞ

To idan aka busa qaho busa xaya



Sura: Suratul Haqqa

Aya : 14

وَحُمِلَتِ ٱلۡأَرۡضُ وَٱلۡجِبَالُ فَدُكَّتَا دَكَّةٗ وَٰحِدَةٗ

Aka kuma xaga qasa da duwatsu sai aka dandaqe su dandaqewa baki xaya