Sura: Suratus Saffat

Aya : 84

إِذۡ جَآءَ رَبَّهُۥ بِقَلۡبٖ سَلِيمٍ

A yayin da ya zo wa Ubangijinsa da lafiyayyar zuciya



Sura: Suratus Saffat

Aya : 85

إِذۡ قَالَ لِأَبِيهِ وَقَوۡمِهِۦ مَاذَا تَعۡبُدُونَ

Lokacin da ya ce da babansa da kuma mutanensa: “Me kuke bauta wa ne?



Sura: Suratus Saffat

Aya : 86

أَئِفۡكًا ءَالِهَةٗ دُونَ ٱللَّهِ تُرِيدُونَ

“Yanzu iyayen giji na qarya ba Allah ba kuke nufi?



Sura: Suratus Saffat

Aya : 87

فَمَا ظَنُّكُم بِرَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

“To mene ne tsammaninku game da Ubangijin talikai?”



Sura: Suratus Saffat

Aya : 88

فَنَظَرَ نَظۡرَةٗ فِي ٱلنُّجُومِ

Sai ya yi duba a cikin taurari, duba na tunani



Sura: Suratus Saffat

Aya : 89

فَقَالَ إِنِّي سَقِيمٞ

Sannan ya ce: “Lalle ni fa ba ni da lafiya.”



Sura: Suratus Saffat

Aya : 90

فَتَوَلَّوۡاْ عَنۡهُ مُدۡبِرِينَ

Sai suka juya daga wurinsa suna masu ba da baya



Sura: Suratus Saffat

Aya : 91

فَرَاغَ إِلَىٰٓ ءَالِهَتِهِمۡ فَقَالَ أَلَا تَأۡكُلُونَ

Sai ya saxaxa zuwa ga gumakansu ya ce (da su): “Yanzu ba za ku ci (abincin da ke gabanku) ba?



Sura: Suratus Saffat

Aya : 92

مَا لَكُمۡ لَا تَنطِقُونَ

“Me ya sa ba kwa yin magana ne?”



Sura: Suratus Saffat

Aya : 93

فَرَاغَ عَلَيۡهِمۡ ضَرۡبَۢا بِٱلۡيَمِينِ

Sai ya yi kansu yana duka da hannunsa na dama



Sura: Suratus Saffat

Aya : 94

فَأَقۡبَلُوٓاْ إِلَيۡهِ يَزِفُّونَ

Sai (mutanensa) suka fuskanto shi suna gaggawa



Sura: Suratus Saffat

Aya : 95

قَالَ أَتَعۡبُدُونَ مَا تَنۡحِتُونَ

Ya ce: “Yanzu kwa riqa bauta wa abin da kuke sassaqawa?



Sura: Suratus Saffat

Aya : 96

وَٱللَّهُ خَلَقَكُمۡ وَمَا تَعۡمَلُونَ

“Alhali kuwa Allah ne Ya halicce ku, da ma abin da kuke aikatawa?”



Sura: Suratus Saffat

Aya : 97

قَالُواْ ٱبۡنُواْ لَهُۥ بُنۡيَٰنٗا فَأَلۡقُوهُ فِي ٱلۡجَحِيمِ

Suka ce: “Ku gina masa wani gini (ku haxa wuta a ciki), sannan ku jefa shi cikin wutar.”



Sura: Suratus Saffat

Aya : 98

فَأَرَادُواْ بِهِۦ كَيۡدٗا فَجَعَلۡنَٰهُمُ ٱلۡأَسۡفَلِينَ

Sai suka yi nufin sa da mugun shiri, sai Muka mayar da su mafiya qasqanci



Sura: Suratus Saffat

Aya : 99

وَقَالَ إِنِّي ذَاهِبٌ إِلَىٰ رَبِّي سَيَهۡدِينِ

Ya kuma ce: “Lalle ni zan yi qaura zuwa ga Ubangijina, zai ko shiryar da ni



Sura: Suratus Saffat

Aya : 100

رَبِّ هَبۡ لِي مِنَ ٱلصَّـٰلِحِينَ

“Ya Ubangijina, Ka yi min baiwa da (xa) ya zama daga (mutane) nagari.”



Sura: Suratus Saffat

Aya : 101

فَبَشَّرۡنَٰهُ بِغُلَٰمٍ حَلِيمٖ

Sai Muka yi masa albishir da yaro mai haquri[1]


1- Shi ne xansa Annabi Isma’il ().


Sura: Suratus Saffat

Aya : 102

فَلَمَّا بَلَغَ مَعَهُ ٱلسَّعۡيَ قَالَ يَٰبُنَيَّ إِنِّيٓ أَرَىٰ فِي ٱلۡمَنَامِ أَنِّيٓ أَذۡبَحُكَ فَٱنظُرۡ مَاذَا تَرَىٰۚ قَالَ يَـٰٓأَبَتِ ٱفۡعَلۡ مَا تُؤۡمَرُۖ سَتَجِدُنِيٓ إِن شَآءَ ٱللَّهُ مِنَ ٱلصَّـٰبِرِينَ

To lokacin da ya kai matsayin yin aiki tare da shi, sai ya ce: “Ya kai xana, lalle na ga ina yanka ka a cikin mafarki, sai ka yi tunani me ka gani?” Sai ya ce: “Ya babana, ka aikata duk abin da aka umarce ka, za ka same ni insha Allahu daga cikin masu haquri.”



Sura: Suratus Saffat

Aya : 103

فَلَمَّآ أَسۡلَمَا وَتَلَّهُۥ لِلۡجَبِينِ

To lokacin da suka sallama wa (Allah), ya kuma kwantar da shi ta xaya gefe na goshinsa (da nufin ya yanka shi)



Sura: Suratus Saffat

Aya : 104

وَنَٰدَيۡنَٰهُ أَن يَـٰٓإِبۡرَٰهِيمُ

Sai Muka kira shi da cewa: “Ya Ibrahimu



Sura: Suratus Saffat

Aya : 105

قَدۡ صَدَّقۡتَ ٱلرُّءۡيَآۚ إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ

“Haqiqa ka gaskata mafarkin.” Lalle Mu kamar haka ne Muke saka wa masu kyautatawa



Sura: Suratus Saffat

Aya : 106

إِنَّ هَٰذَا لَهُوَ ٱلۡبَلَـٰٓؤُاْ ٱلۡمُبِينُ

Lalle wannan tabbas shi ne bala’i qarara



Sura: Suratus Saffat

Aya : 107

وَفَدَيۡنَٰهُ بِذِبۡحٍ عَظِيمٖ

Muka kuma fanshe shi da abin yankawa mai girma



Sura: Suratus Saffat

Aya : 108

وَتَرَكۡنَا عَلَيۡهِ فِي ٱلۡأٓخِرِينَ

Muka kuma bar (kyakkyawan yabo) a gare shi ga ‘yan baya



Sura: Suratus Saffat

Aya : 109

سَلَٰمٌ عَلَىٰٓ إِبۡرَٰهِيمَ

Aminci ya tabbata ga Ibrahimu



Sura: Suratus Saffat

Aya : 110

كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ

Kamar haka ne Muke saka wa masu kyautatawa



Sura: Suratus Saffat

Aya : 111

إِنَّهُۥ مِنۡ عِبَادِنَا ٱلۡمُؤۡمِنِينَ

Lalle shi yana daga cikin bayinmu muminai



Sura: Suratus Saffat

Aya : 112

وَبَشَّرۡنَٰهُ بِإِسۡحَٰقَ نَبِيّٗا مِّنَ ٱلصَّـٰلِحِينَ

Muka kuma yi masa albishir da Is’haqa a matsayin Annabi daga salihai



Sura: Suratus Saffat

Aya : 113

وَبَٰرَكۡنَا عَلَيۡهِ وَعَلَىٰٓ إِسۡحَٰقَۚ وَمِن ذُرِّيَّتِهِمَا مُحۡسِنٞ وَظَالِمٞ لِّنَفۡسِهِۦ مُبِينٞ

Muka kuma yi masa albarka, da kuma Is’haqa. Daga zuriyarsu kuma akwai mai kyautatawa akwai kuma mai zaluntar kansa a fili (wato kafiri)