Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 201

لَا يُؤۡمِنُونَ بِهِۦ حَتَّىٰ يَرَوُاْ ٱلۡعَذَابَ ٱلۡأَلِيمَ

Ba za su yi imani da shi ba har sai sun ga azaba mai raxaxi



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 202

فَيَأۡتِيَهُم بَغۡتَةٗ وَهُمۡ لَا يَشۡعُرُونَ

Sannan (azabar) za ta zo musu ba zato ba tsammani, ba tare da suna sane ba



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 203

فَيَقُولُواْ هَلۡ نَحۡنُ مُنظَرُونَ

Sai su ce: “Yanzu za a saurara mana?”



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 204

أَفَبِعَذَابِنَا يَسۡتَعۡجِلُونَ

Yanzu azabarmu suke neman gaggautowa?



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 205

أَفَرَءَيۡتَ إِن مَّتَّعۡنَٰهُمۡ سِنِينَ

Ka ba Ni labari idan Muka jiyar da su daxi na tsawon shekaru



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 206

ثُمَّ جَآءَهُم مَّا كَانُواْ يُوعَدُونَ

Sannan kuma abin da ake yi musu alkawarin narko da shi ya zo musu



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 207

مَآ أَغۡنَىٰ عَنۡهُم مَّا كَانُواْ يُمَتَّعُونَ

Abin da ake jiyar da su daxi a da ba zai amfana musu komai ba



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 208

وَمَآ أَهۡلَكۡنَا مِن قَرۡيَةٍ إِلَّا لَهَا مُنذِرُونَ

Ba Mu tava hallaka wata al’umma ba face sai ta samu masu yi mata gargaxi



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 209

ذِكۡرَىٰ وَمَا كُنَّا ظَٰلِمِينَ

(Wannan) tunatarwa ce (gare su), ba Mu kuwa kasance azzalumai ba



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 210

وَمَا تَنَزَّلَتۡ بِهِ ٱلشَّيَٰطِينُ

Kuma shaixanu ba su sauko da shi ba



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 211

وَمَا يَنۢبَغِي لَهُمۡ وَمَا يَسۡتَطِيعُونَ

Kuma bai kamace su ba, ba kuma za su iya ba



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 212

إِنَّهُمۡ عَنِ ٱلسَّمۡعِ لَمَعۡزُولُونَ

Lalle su ababen kangewa ne daga jin (wahayi)



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 213

فَلَا تَدۡعُ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَ فَتَكُونَ مِنَ ٱلۡمُعَذَّبِينَ

To kada ka bauta wa wani tare da Allah, sai ka zamanto daga waxanda za a yi wa azaba



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 214

وَأَنذِرۡ عَشِيرَتَكَ ٱلۡأَقۡرَبِينَ

Kuma ka gargaxi danginka mafiya kusanci



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 215

وَٱخۡفِضۡ جَنَاحَكَ لِمَنِ ٱتَّبَعَكَ مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ

Ka kuma tausasa ga wanda ya bi ka daga muminai



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 216

فَإِنۡ عَصَوۡكَ فَقُلۡ إِنِّي بَرِيٓءٞ مِّمَّا تَعۡمَلُونَ

To idan suka sava maka sai ka ce: “Ni lalle ba ruwana da abin da kuke aikatawa.”



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 217

وَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱلۡعَزِيزِ ٱلرَّحِيمِ

Ka kuma dogara ga Mabuwayi, Mai rahama



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 218

ٱلَّذِي يَرَىٰكَ حِينَ تَقُومُ

Wanda Yake ganin ka yayin da kake tashi (don yin salla)



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 219

وَتَقَلُّبَكَ فِي ٱلسَّـٰجِدِينَ

Da kuma (yayin) jujjuyawarka cikin masu sujjada[1]


1- Watau masallata a sallar jam’i.


Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 220

إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ

Haqiqa Shi Mai ji ne, Masani



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 221

هَلۡ أُنَبِّئُكُمۡ عَلَىٰ مَن تَنَزَّلُ ٱلشَّيَٰطِينُ

Shin ba Na ba ku labari ba game da wanda shexanu suke saukar masa?



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 222

تَنَزَّلُ عَلَىٰ كُلِّ أَفَّاكٍ أَثِيمٖ

Suna sauka ne a kan duk wani maqaryaci mai yawan laifi



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 223

يُلۡقُونَ ٱلسَّمۡعَ وَأَكۡثَرُهُمۡ كَٰذِبُونَ

Suna jefa wa (bokaye) abin da suka sato jinsa, yawancinsu kuwa maqaryata ne



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 224

وَٱلشُّعَرَآءُ يَتَّبِعُهُمُ ٱلۡغَاوُۥنَ

Mawaqa kuwa vatattu ne suke bin su



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 225

أَلَمۡ تَرَ أَنَّهُمۡ فِي كُلِّ وَادٖ يَهِيمُونَ

Ba ka ga cewa su kutsawa suke yi cikin kowanne kwari ba[1]?


1- Watau suna kutsawa cikin kowane saqo-saqo na waqe-waqe, wani lokaci ta hanyar yabo, wani lokaci kuma ya hanyar zambo ko alfahari, su faxi qarya da gaskiya.


Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 226

وَأَنَّهُمۡ يَقُولُونَ مَا لَا يَفۡعَلُونَ

Lalle kuma suna faxar abin da ba sa aikatawa



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 227

إِلَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ وَذَكَرُواْ ٱللَّهَ كَثِيرٗا وَٱنتَصَرُواْ مِنۢ بَعۡدِ مَا ظُلِمُواْۗ وَسَيَعۡلَمُ ٱلَّذِينَ ظَلَمُوٓاْ أَيَّ مُنقَلَبٖ يَنقَلِبُونَ

Sai dai waxanda suka yi imani kuma suka yi aiki nagari, kuma suka ambaci Allah da yawa, suka kuma yi sakayya bayan an zalunce su[1]. Waxanda suka yi zalunci kuwa ba da daxewa ba za su san kowace makomar za su koma


1- Watau mawaqan Musulmi waxanda suke mayar da martani a kan mawaqan kafirai masu sukan Musulunci.


Sura: Suratun Namli

Aya : 1

طسٓۚ تِلۡكَ ءَايَٰتُ ٱلۡقُرۡءَانِ وَكِتَابٖ مُّبِينٍ

XA SIN[1]. Waxannan ayoyin Alqur’ani ne kuma Littafi mabayyani


1- Duba Suratul Baqara, aya ta 1, hashiya ta 8.


Sura: Suratun Namli

Aya : 2

هُدٗى وَبُشۡرَىٰ لِلۡمُؤۡمِنِينَ

(Kuma) shiriya da albishir ne ga muminai



Sura: Suratun Namli

Aya : 3

ٱلَّذِينَ يُقِيمُونَ ٱلصَّلَوٰةَ وَيُؤۡتُونَ ٱلزَّكَوٰةَ وَهُم بِٱلۡأٓخِرَةِ هُمۡ يُوقِنُونَ

Waxanda suke tsai da salla, suke kuma ba da zakka suna masu sakankancewa da ranar lahira