Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 94

فَكُبۡكِبُواْ فِيهَا هُمۡ وَٱلۡغَاوُۥنَ

Sai aka kikkifa su cikinta (wutar) su da vatattu



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 95

وَجُنُودُ إِبۡلِيسَ أَجۡمَعُونَ

Da kuma rundunar Iblis gaba xaya



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 96

قَالُواْ وَهُمۡ فِيهَا يَخۡتَصِمُونَ

Sai suka ce, alhali suna jayayya da juna a cikinta:



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 97

تَٱللَّهِ إِن كُنَّا لَفِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٍ

“Mun rantse da Allah tabbas mun kasance (a duniya) cikin vata bayyananne



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 98

إِذۡ نُسَوِّيكُم بِرَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

“Lokacin da muke daidaita ku da Ubangijin talikai[1]


1- Watau wajen soyayya da bauta.


Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 99

وَمَآ أَضَلَّنَآ إِلَّا ٱلۡمُجۡرِمُونَ

“Ba kuwa waxanda suka vatar da mu sai manyan masu laifuka



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 100

فَمَا لَنَا مِن شَٰفِعِينَ

“To a (yau) ba mu da wasu masu ceto



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 101

وَلَا صَدِيقٍ حَمِيمٖ

“Ba kuma wani aboki na qut-da-qut



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 102

فَلَوۡ أَنَّ لَنَا كَرَّةٗ فَنَكُونَ مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ

“To ina ma da za mu samu damar komawa, sai mu zamanto daga muminai!”



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 103

إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ

Lalle a game da wannan tabbas akwai aya; kuma yawancinsu, ba su zamanto muminai ba



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 104

وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ

Kuma lalle Ubangijinka tabbas Shi ne Mabuwayi Mai jin qai



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 105

كَذَّبَتۡ قَوۡمُ نُوحٍ ٱلۡمُرۡسَلِينَ

Mutanen Nuhu sun qaryata mazanni[1]


1- Domin qaryata Annabi Nuhu () daidai yake da qaryata dukkan manzannin Allah, domin saqo iri xaya suke xauke da shi.


Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 106

إِذۡ قَالَ لَهُمۡ أَخُوهُمۡ نُوحٌ أَلَا تَتَّقُونَ

Lokacin da xan’uwansu Nuhu ya ce da su: “Yanzu ba za ku kiyaye dokokin Allah ba?



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 107

إِنِّي لَكُمۡ رَسُولٌ أَمِينٞ

“Lalle ni Manzo ne amintacce a gare ku



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 108

فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ

“To ku kiyaye dokokin Allah kuma ku bi ni



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 109

وَمَآ أَسۡـَٔلُكُمۡ عَلَيۡهِ مِنۡ أَجۡرٍۖ إِنۡ أَجۡرِيَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

“Ba na kuma tambayar ku wani lada a game da shi (isar da manzancin). Ladana yana wajen Ubangijin talikai kawai



Sura: Suratus Shu’ara

Aya : 110

فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ

“To ku kiyaye dokokin Allah kuma ku bi ni.”