Sura: Suratu Maryam

Aya : 31

وَجَعَلَنِي مُبَارَكًا أَيۡنَ مَا كُنتُ وَأَوۡصَٰنِي بِٱلصَّلَوٰةِ وَٱلزَّكَوٰةِ مَا دُمۡتُ حَيّٗا

“Ya kuma sanya ni mai albarka a duk inda nake, kuma Ya umarce ni da yin salla da kuma ba da zakka matuqar ina raye



Sura: Suratu Maryam

Aya : 32

وَبَرَّۢا بِوَٰلِدَتِي وَلَمۡ يَجۡعَلۡنِي جَبَّارٗا شَقِيّٗا

“Kuma mai biyayya ga mahaifiyata, bai kuma sanya ni mai girman kai mai savo ba



Sura: Suratu Maryam

Aya : 33

وَٱلسَّلَٰمُ عَلَيَّ يَوۡمَ وُلِدتُّ وَيَوۡمَ أَمُوتُ وَيَوۡمَ أُبۡعَثُ حَيّٗا

“Amincin (Allah) kuma ya tabbata a gare ni ranar da aka haife ni da ranar da zan mutu da kuma ranar da za a tashe ni rayayye.”



Sura: Suratu Maryam

Aya : 34

ذَٰلِكَ عِيسَى ٱبۡنُ مَرۡيَمَۖ قَوۡلَ ٱلۡحَقِّ ٱلَّذِي فِيهِ يَمۡتَرُونَ

Wannan shi ne Isa xan Maryamu. Zance na gaskiya wanda a kansa ne suke ta shakka suna jayayya (da junansu)



Sura: Suratu Maryam

Aya : 35

مَا كَانَ لِلَّهِ أَن يَتَّخِذَ مِن وَلَدٖۖ سُبۡحَٰنَهُۥٓۚ إِذَا قَضَىٰٓ أَمۡرٗا فَإِنَّمَا يَقُولُ لَهُۥ كُن فَيَكُونُ

Ba zai yiwu a ce Allah yana da xa ba; tsarki ya tabbata a gare Shi. Idan Ya nufi zartar da wani lamari sai kawai Ya ce masa: “Kasance”, sai ko ya kasance



Sura: Suratu Maryam

Aya : 36

وَإِنَّ ٱللَّهَ رَبِّي وَرَبُّكُمۡ فَٱعۡبُدُوهُۚ هَٰذَا صِرَٰطٞ مُّسۡتَقِيمٞ

“Lalle kuma Allah shi ne Ubangijina kuma Ubangijinku, sai ku bauta masa. Wannan ita ce hanya madaidaiciya.”



Sura: Suratu Maryam

Aya : 37

فَٱخۡتَلَفَ ٱلۡأَحۡزَابُ مِنۢ بَيۡنِهِمۡۖ فَوَيۡلٞ لِّلَّذِينَ كَفَرُواْ مِن مَّشۡهَدِ يَوۡمٍ عَظِيمٍ

Sai qungiyoyin suka sassava a tsakaninsu; to bone ya tabbata ga waxanda suka kafirta daga halartar rana mai girma (ita ce alqiyama)



Sura: Suratu Maryam

Aya : 38

أَسۡمِعۡ بِهِمۡ وَأَبۡصِرۡ يَوۡمَ يَأۡتُونَنَا لَٰكِنِ ٱلظَّـٰلِمُونَ ٱلۡيَوۡمَ فِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٖ

Ka yi mamakin jinsu da ganinsu a ranar da za su zo mana; sai dai azzalumai a wannan rana suna cikin vata mabayyani



Sura: Suratu Maryam

Aya : 39

وَأَنذِرۡهُمۡ يَوۡمَ ٱلۡحَسۡرَةِ إِذۡ قُضِيَ ٱلۡأَمۡرُ وَهُمۡ فِي غَفۡلَةٖ وَهُمۡ لَا يُؤۡمِنُونَ

Ka kuma gargaxe su game da ranar nadama, lokacin da aka qare hisabi, alhali kuwa su (a duniya) suna cikin rafkana kuma su ba sa yin imani



Sura: Suratu Maryam

Aya : 40

إِنَّا نَحۡنُ نَرِثُ ٱلۡأَرۡضَ وَمَنۡ عَلَيۡهَا وَإِلَيۡنَا يُرۡجَعُونَ

Lalle Mu ne za Mu gaje qasa da wanda yake bayanta kuma gare Mu ne za a komar da su



Sura: Suratu Maryam

Aya : 41

وَٱذۡكُرۡ فِي ٱلۡكِتَٰبِ إِبۡرَٰهِيمَۚ إِنَّهُۥ كَانَ صِدِّيقٗا نَّبِيًّا

Kuma ka ambaci (labarin) Ibrahimu a cikin (wannan) littafi (Alqur’ani). Lalle shi mutum ne mai yawan gaskiya (kuma) Annabi



Sura: Suratu Maryam

Aya : 42

إِذۡ قَالَ لِأَبِيهِ يَـٰٓأَبَتِ لِمَ تَعۡبُدُ مَا لَا يَسۡمَعُ وَلَا يُبۡصِرُ وَلَا يُغۡنِي عَنكَ شَيۡـٔٗا

Lokacin da ya ce da Babansa: “Ya Babana, me ya sa kake bauta wa abin da ba ya ji ba kuma ya gani, kuma ba ya yi maka maganin komai?



Sura: Suratu Maryam

Aya : 43

يَـٰٓأَبَتِ إِنِّي قَدۡ جَآءَنِي مِنَ ٱلۡعِلۡمِ مَا لَمۡ يَأۡتِكَ فَٱتَّبِعۡنِيٓ أَهۡدِكَ صِرَٰطٗا سَوِيّٗا

“Ya Babana, Lalle ni haqiqa wani ilimi ya zo mini wanda kai bai zo maka ba, to ka bi ni zan shiryar da kai hanya madaidaiciya



Sura: Suratu Maryam

Aya : 44

يَـٰٓأَبَتِ لَا تَعۡبُدِ ٱلشَّيۡطَٰنَۖ إِنَّ ٱلشَّيۡطَٰنَ كَانَ لِلرَّحۡمَٰنِ عَصِيّٗا

“Ya Babana, kada ka bauta wa Shaixan ; lalle Shaixan ya kasance mai savo ne ga (Allah) Mai rahama



Sura: Suratu Maryam

Aya : 45

يَـٰٓأَبَتِ إِنِّيٓ أَخَافُ أَن يَمَسَّكَ عَذَابٞ مِّنَ ٱلرَّحۡمَٰنِ فَتَكُونَ لِلشَّيۡطَٰنِ وَلِيّٗا

“Ya Babana, lalle ni fa ina tsoron azaba ta shafe ka daga (Allah) Mai rahama, sai ka zama majivincin Shaixan.”



Sura: Suratu Maryam

Aya : 46

قَالَ أَرَاغِبٌ أَنتَ عَنۡ ءَالِهَتِي يَـٰٓإِبۡرَٰهِيمُۖ لَئِن لَّمۡ تَنتَهِ لَأَرۡجُمَنَّكَۖ وَٱهۡجُرۡنِي مَلِيّٗا

(Babansa) ya ce: “Yanzu Ibrahimu qyamar iyayen gijina kake yi? To tabbas idan ba ka bari ba lalle zan jefe ka; ka vace min da gani na tsawon lokaci!”



Sura: Suratu Maryam

Aya : 47

قَالَ سَلَٰمٌ عَلَيۡكَۖ سَأَسۡتَغۡفِرُ لَكَ رَبِّيٓۖ إِنَّهُۥ كَانَ بِي حَفِيّٗا

(Annabi Ibrahimu) ya ce: “Aminci ya tabbata gare ka; zan nema maka gafarar Ubangijina[1]; don ko lalle Shi ya tabbata Mai haba-haba ne da ni


1- Ya faxi haka ne kafin Allah ya hana shi nema masa gafara.


Sura: Suratu Maryam

Aya : 48

وَأَعۡتَزِلُكُمۡ وَمَا تَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَأَدۡعُواْ رَبِّي عَسَىٰٓ أَلَّآ أَكُونَ بِدُعَآءِ رَبِّي شَقِيّٗا

“Zan kuwa qaurace muku ku da abin da kuke bauta wa wanda ba Allah ba, in kuma roqi Ubangijina, na kuma sa tsammanin cewa ba zan zama tavavve ba game da roqon Ubangijina.”



Sura: Suratu Maryam

Aya : 49

فَلَمَّا ٱعۡتَزَلَهُمۡ وَمَا يَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَهَبۡنَا لَهُۥٓ إِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَۖ وَكُلّٗا جَعَلۡنَا نَبِيّٗا

To lokacin da ya qaurace musu tare da abin da suke bauta wa wanda ba Allah ba, sai Muka yi masa baiwa da Is’haqa da Ya’aqubu; kowannensu kuma Muka ba shi annabta



Sura: Suratu Maryam

Aya : 50

وَوَهَبۡنَا لَهُم مِّن رَّحۡمَتِنَا وَجَعَلۡنَا لَهُمۡ لِسَانَ صِدۡقٍ عَلِيّٗا

Muka kuma yi musu baiwa da rahamarmu, kuma Muka sanya musu kyakkyawan ambato maxaukaki[1]


1- Watau ya sa suka zamanto ababen yabo mai xorewa a gun kowa.


Sura: Suratu Maryam

Aya : 51

وَٱذۡكُرۡ فِي ٱلۡكِتَٰبِ مُوسَىٰٓۚ إِنَّهُۥ كَانَ مُخۡلَصٗا وَكَانَ رَسُولٗا نَّبِيّٗا

Ka kuma ambaci (labarin) Musa cikin (wannan) Littafi (Alqur’ani). Lalle shi zavavve ne, ya kuma kasance Annabi ne Manzo



Sura: Suratu Maryam

Aya : 52

وَنَٰدَيۡنَٰهُ مِن جَانِبِ ٱلطُّورِ ٱلۡأَيۡمَنِ وَقَرَّبۡنَٰهُ نَجِيّٗا

Muka kuma kira shi a gefen dutsen Xuri na dama, Muka kuma kusanto shi yana mai ganawa (da Mu)



Sura: Suratu Maryam

Aya : 53

وَوَهَبۡنَا لَهُۥ مِن رَّحۡمَتِنَآ أَخَاهُ هَٰرُونَ نَبِيّٗا

Kuma cikin rahamarmu Muka yi masa baiwa da xan’uwansa Haruna (shi ma) Annabi



Sura: Suratu Maryam

Aya : 54

وَٱذۡكُرۡ فِي ٱلۡكِتَٰبِ إِسۡمَٰعِيلَۚ إِنَّهُۥ كَانَ صَادِقَ ٱلۡوَعۡدِ وَكَانَ رَسُولٗا نَّبِيّٗا

Kuma ka ambaci (labarin) Isma’ila a cikin (wannan) Littafi (Alqur’ani). Lalle shi ya kasance mai gaskiyar alqawari ne, kuma ya kasance Annabi ne, Manzo



Sura: Suratu Maryam

Aya : 55

وَكَانَ يَأۡمُرُ أَهۡلَهُۥ بِٱلصَّلَوٰةِ وَٱلزَّكَوٰةِ وَكَانَ عِندَ رَبِّهِۦ مَرۡضِيّٗا

Kuma ya zamanto yana umartar iyalinsa da (tsai da) salla da kuma (ba da) zakka, kuma shi yardajje ne a wurin Ubangijinsa



Sura: Suratu Maryam

Aya : 56

وَٱذۡكُرۡ فِي ٱلۡكِتَٰبِ إِدۡرِيسَۚ إِنَّهُۥ كَانَ صِدِّيقٗا نَّبِيّٗا

Kuma ka ambaci (labarin) Idrisu a cikin (wannan) Littafi (Alqur’ani). Lalle shi ya kasance mai yawan gaskiya ne, Annabi



Sura: Suratu Maryam

Aya : 57

وَرَفَعۡنَٰهُ مَكَانًا عَلِيًّا

Muka kuma xaukaka shi daraja maxaukakiya[1]


1- A Mi’iraji da Annabi () ya yi ya haxu da shi a sama ta huxu.


Sura: Suratu Maryam

Aya : 58

أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ أَنۡعَمَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِم مِّنَ ٱلنَّبِيِّـۧنَ مِن ذُرِّيَّةِ ءَادَمَ وَمِمَّنۡ حَمَلۡنَا مَعَ نُوحٖ وَمِن ذُرِّيَّةِ إِبۡرَٰهِيمَ وَإِسۡرَـٰٓءِيلَ وَمِمَّنۡ هَدَيۡنَا وَٱجۡتَبَيۡنَآۚ إِذَا تُتۡلَىٰ عَلَيۡهِمۡ ءَايَٰتُ ٱلرَّحۡمَٰنِ خَرُّواْۤ سُجَّدٗاۤ وَبُكِيّٗا۩

Waxannan su ne annabawa waxanda Allah Ya yi ni’ima a gare su, daga zuriyar Adamu, da kuma waxanda Muka xauko (a jirgin ruwa) tare da Nuhu, daga kuma zuriyar Ibrahimu da Isra’ila (watau Ya’aqubu), da kuma waxanda Muka shiryar da su Muka kuma zave su. Idan ana karanta musu ayoyin (Allah) Mai rahama sai su faxi su yi sujjada suna kuka



Sura: Suratu Maryam

Aya : 59

۞فَخَلَفَ مِنۢ بَعۡدِهِمۡ خَلۡفٌ أَضَاعُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَٱتَّبَعُواْ ٱلشَّهَوَٰتِۖ فَسَوۡفَ يَلۡقَوۡنَ غَيًّا

Sai wasu suka maye gurbinsu bayansu waxanda suka tozarta salla suka kuma bi sha’awace-sha’awacen (duniya na savo); to ba da daxewa ba za su haxu da mummunan sharri (a Jahannama)



Sura: Suratu Maryam

Aya : 60

إِلَّا مَن تَابَ وَءَامَنَ وَعَمِلَ صَٰلِحٗا فَأُوْلَـٰٓئِكَ يَدۡخُلُونَ ٱلۡجَنَّةَ وَلَا يُظۡلَمُونَ شَيۡـٔٗا

Sai dai wanda ya tuba ya yi imani ya kuma yi aiki na gari, to waxannan za su shiga Aljanna, kuma ba za a tauye musu komai ba