قَالَ فَأۡتِ بِهِۦٓ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّـٰدِقِينَ
(Fir’auna) ya ce: “To ka zo da shi xin in ka kasance daga masu gaskiya.”
فَأَلۡقَىٰ عَصَاهُ فَإِذَا هِيَ ثُعۡبَانٞ مُّبِينٞ
Sannan (Musa) ya jefa sandarsa sai ga ta (ta zama) kumurci quru-quru
وَنَزَعَ يَدَهُۥ فَإِذَا هِيَ بَيۡضَآءُ لِلنَّـٰظِرِينَ
Ya kuma zaro hannunsa (daga cikin rigarsa) sai ga shi fari fat ga masu gani
قَالَ لِلۡمَلَإِ حَوۡلَهُۥٓ إِنَّ هَٰذَا لَسَٰحِرٌ عَلِيمٞ
(Sai Fir’auna) ya ce da manyan mutanen da ke kewaye da shi: “Lalle wannan tabbas mai sihiri ne qwararre
يُرِيدُ أَن يُخۡرِجَكُم مِّنۡ أَرۡضِكُم بِسِحۡرِهِۦ فَمَاذَا تَأۡمُرُونَ
“Yana nufi ne ya fitar da ku daga qasarku da sihirinsa, to da me za ku yi umarni?”
قَالُوٓاْ أَرۡجِهۡ وَأَخَاهُ وَٱبۡعَثۡ فِي ٱلۡمَدَآئِنِ حَٰشِرِينَ
Suka ce: “Ka dakatar da shi tare da xan’uwansa, kuma ka aika manzanni cikin birane su tattaro maka (masu sihiri)
يَأۡتُوكَ بِكُلِّ سَحَّارٍ عَلِيمٖ
“Su zo maka da duk wani mai sihiri qwararre.”
فَجُمِعَ ٱلسَّحَرَةُ لِمِيقَٰتِ يَوۡمٖ مَّعۡلُومٖ
Sai aka tattara masu sihirin (don su zo) a qayyadajjiyar rana sananniya[1]
1- Watau ranar bikin idinsu.
وَقِيلَ لِلنَّاسِ هَلۡ أَنتُم مُّجۡتَمِعُونَ
Aka kuma ce da mutane: “Shin za ku tattaru
لَعَلَّنَا نَتَّبِعُ ٱلسَّحَرَةَ إِن كَانُواْ هُمُ ٱلۡغَٰلِبِينَ
“Don mu goyi bayan masu sihiri idan har sun kasance su ne masu galaba?”
فَلَمَّا جَآءَ ٱلسَّحَرَةُ قَالُواْ لِفِرۡعَوۡنَ أَئِنَّ لَنَا لَأَجۡرًا إِن كُنَّا نَحۡنُ ٱلۡغَٰلِبِينَ
Sannan lokacin da masu sihirin suka zo sai suka ce da Fir’auna: “Shin muna da wani lada (da za ka ba mu) in har mun zama mu ne masu galaba?”
قَالَ نَعَمۡ وَإِنَّكُمۡ إِذٗا لَّمِنَ ٱلۡمُقَرَّبِينَ
(Fir’auna) ya ce: “Na’am, kuma ma idan haka ya faru, to tabbas za ku zama daga makusanta.”
قَالَ لَهُم مُّوسَىٰٓ أَلۡقُواْ مَآ أَنتُم مُّلۡقُونَ
(Sai Musa) ya ce da su: “Ku jefa duk abin da za ku jefa.”
فَأَلۡقَوۡاْ حِبَالَهُمۡ وَعِصِيَّهُمۡ وَقَالُواْ بِعِزَّةِ فِرۡعَوۡنَ إِنَّا لَنَحۡنُ ٱلۡغَٰلِبُونَ
Sai suka jefa igiyoyinsu da sandunansu suka kuma ce: “Lalle da izzar Fir’auna tabbas mu ne masu galaba.”
فَأَلۡقَىٰ مُوسَىٰ عَصَاهُ فَإِذَا هِيَ تَلۡقَفُ مَا يَأۡفِكُونَ
Sai Musa ya jefa sandarsa, sai ga ta tana lanqwame duk abin da suke qagowa (na sihiri)
فَأُلۡقِيَ ٱلسَّحَرَةُ سَٰجِدِينَ
Sai aka durqusar da masu sihirin suna masu sujjada
قَالُوٓاْ ءَامَنَّا بِرَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Suka ce: “Mun yi imani da Ubangijin talikai
رَبِّ مُوسَىٰ وَهَٰرُونَ
“Ubangijin Musa da Haruna.”
قَالَ ءَامَنتُمۡ لَهُۥ قَبۡلَ أَنۡ ءَاذَنَ لَكُمۡۖ إِنَّهُۥ لَكَبِيرُكُمُ ٱلَّذِي عَلَّمَكُمُ ٱلسِّحۡرَ فَلَسَوۡفَ تَعۡلَمُونَۚ لَأُقَطِّعَنَّ أَيۡدِيَكُمۡ وَأَرۡجُلَكُم مِّنۡ خِلَٰفٖ وَلَأُصَلِّبَنَّكُمۡ أَجۡمَعِينَ
(Sai Fir’auna) ya ce: “Yanzu kwa yi imani da shi tun kafin in ba ku izini? Lalle tabbas shi ne babbanku wanda ya koya muku sihiri; to tabbas kuwa kwa sani. Lalle zan yanyanke hannayenku da qafafuwanku a tarnaqe, kuma tabbas zan gicciye ku gaba xaya!”
قَالُواْ لَا ضَيۡرَۖ إِنَّآ إِلَىٰ رَبِّنَا مُنقَلِبُونَ
Sai suka ce: “Ai ba damuwa; lalle mu masu komawa ne zuwa ga Ubangijinmu
إِنَّا نَطۡمَعُ أَن يَغۡفِرَ لَنَا رَبُّنَا خَطَٰيَٰنَآ أَن كُنَّآ أَوَّلَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
“Lalle mu muna kwaxayin Ubangijinmu Ya gafarta mana kurakuranmu saboda zamantowarmu farkon muminai.”
۞وَأَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰ مُوسَىٰٓ أَنۡ أَسۡرِ بِعِبَادِيٓ إِنَّكُم مُّتَّبَعُونَ
Muka kuma yi wa Musa wahayi cewa: “Ka tafi cikin dare tare da bayina, lalle ku za a biyo bayanku.”
فَأَرۡسَلَ فِرۡعَوۡنُ فِي ٱلۡمَدَآئِنِ حَٰشِرِينَ
Sai Fir’auna ya aika zuwa birane don a tattaro (mayaqa)
إِنَّ هَـٰٓؤُلَآءِ لَشِرۡذِمَةٞ قَلِيلُونَ
(Fir’auna yana cewa): “Lalle waxannan tabbas ‘yan tsirarin jama’a ne
وَإِنَّهُمۡ لَنَا لَغَآئِظُونَ
“Kuma haqiqa su lalle suna fusata mu
وَإِنَّا لَجَمِيعٌ حَٰذِرُونَ
“Lalle kuma mu tabbas gaba xayanmu masu kwana cikin shiri ne.”
فَأَخۡرَجۡنَٰهُم مِّن جَنَّـٰتٖ وَعُيُونٖ
(Allah Ya ce): Sai Muka fitar da su daga gonaki da kuma idandunan ruwa
وَكُنُوزٖ وَمَقَامٖ كَرِيمٖ
Da taskoki da kuma mazauni na alfarma
كَذَٰلِكَۖ وَأَوۡرَثۡنَٰهَا بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ
Kamar haka ne Muka gadar da su ga Banu-Isra’ila
فَأَتۡبَعُوهُم مُّشۡرِقِينَ
Sai suka bi bayansu a lokacin fitowar rana