Sura: Suratul Furqan

Aya : 61

تَبَارَكَ ٱلَّذِي جَعَلَ فِي ٱلسَّمَآءِ بُرُوجٗا وَجَعَلَ فِيهَا سِرَٰجٗا وَقَمَرٗا مُّنِيرٗا

Wanda Ya sanya wuraren saukar taurari cikin sama, Ya kuma sanya mata rana mai haske da wata mai haskakawa[1], albarkatunsa sun yawaita


1- Watau rana mai xauke da haske a karan-kanta da kuma wata wanda yake samun haskensa daga hasken rana.


Sura: Suratul Furqan

Aya : 62

وَهُوَ ٱلَّذِي جَعَلَ ٱلَّيۡلَ وَٱلنَّهَارَ خِلۡفَةٗ لِّمَنۡ أَرَادَ أَن يَذَّكَّرَ أَوۡ أَرَادَ شُكُورٗا

Shi ne kuma wanda Ya sanya dare da rana masu maye wa juna ga wanda ya yi nufin ya wa’azantu ko kuma ya yi nufin godiya



Sura: Suratul Furqan

Aya : 63

وَعِبَادُ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلَّذِينَ يَمۡشُونَ عَلَى ٱلۡأَرۡضِ هَوۡنٗا وَإِذَا خَاطَبَهُمُ ٱلۡجَٰهِلُونَ قَالُواْ سَلَٰمٗا

Bayin (Allah) Mai rahama kuwa (su ne) waxanda suke tafiya a bayan qasa a natse; idan kuma wawaye sun yi musu magana (sai) su faxa (musu) magana ta aminci



Sura: Suratul Furqan

Aya : 64

وَٱلَّذِينَ يَبِيتُونَ لِرَبِّهِمۡ سُجَّدٗا وَقِيَٰمٗا

(Su ne) kuma waxanda suke kwana suna masu sujjada da tsayuwa ga Ubangijinsu



Sura: Suratul Furqan

Aya : 65

وَٱلَّذِينَ يَقُولُونَ رَبَّنَا ٱصۡرِفۡ عَنَّا عَذَابَ جَهَنَّمَۖ إِنَّ عَذَابَهَا كَانَ غَرَامًا

(Su ne) kuma waxanda suke cewa: “Ya Ubangijinmu, Ka kawar mana da azabar Jahannama; lalle azabarta ta kasance halaka ce mai xorewa



Sura: Suratul Furqan

Aya : 66

إِنَّهَا سَآءَتۡ مُسۡتَقَرّٗا وَمُقَامٗا

“Lalle ita (Jahannama) ta kasance mummunar matabbata kuma mazauna (ga kafirai).”



Sura: Suratul Furqan

Aya : 67

وَٱلَّذِينَ إِذَآ أَنفَقُواْ لَمۡ يُسۡرِفُواْ وَلَمۡ يَقۡتُرُواْ وَكَانَ بَيۡنَ ذَٰلِكَ قَوَامٗا

(Su ne) kuma waxanda idan suka ciyar ba sa almubazzaranci kuma ba sa yin qwauro, (ciyarwarsu) kuwa ta kasance tsaka-tsaki ce



Sura: Suratul Furqan

Aya : 68

وَٱلَّذِينَ لَا يَدۡعُونَ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَ وَلَا يَقۡتُلُونَ ٱلنَّفۡسَ ٱلَّتِي حَرَّمَ ٱللَّهُ إِلَّا بِٱلۡحَقِّ وَلَا يَزۡنُونَۚ وَمَن يَفۡعَلۡ ذَٰلِكَ يَلۡقَ أَثَامٗا

(Su ne) kuma waxanda ba sa bauta wa wani tare da Allah, kuma ba sa kashe ran da Allah Ya hana kashewa sai da haqqi, kuma ba sa yin zina. Wanda kuwa ya aikata hakan to zai haxu da (uqubar) laifinsa



Sura: Suratul Furqan

Aya : 69

يُضَٰعَفۡ لَهُ ٱلۡعَذَابُ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ وَيَخۡلُدۡ فِيهِۦ مُهَانًا

Za a ninninka masa azaba ranar alqiyama, kuma ya dawwama a cikinta a wulaqance



Sura: Suratul Furqan

Aya : 70

إِلَّا مَن تَابَ وَءَامَنَ وَعَمِلَ عَمَلٗا صَٰلِحٗا فَأُوْلَـٰٓئِكَ يُبَدِّلُ ٱللَّهُ سَيِّـَٔاتِهِمۡ حَسَنَٰتٖۗ وَكَانَ ٱللَّهُ غَفُورٗا رَّحِيمٗا

Sai dai wanda ya tuba ya kuma yi imani, kuma ya yi aiki na gari, to waxannan Allah zai musanya munanan ayyukansu da kyawawa. Allah kuwa ya kasance Mai gafara ne, Mai jin qai



Sura: Suratul Furqan

Aya : 71

وَمَن تَابَ وَعَمِلَ صَٰلِحٗا فَإِنَّهُۥ يَتُوبُ إِلَى ٱللَّهِ مَتَابٗا

Wanda kuwa ya tuba ya kuma yi aiki na gari, to lalle shi ne wanda yake tuba na gaskiya zuwa ga Allah



Sura: Suratul Furqan

Aya : 72

وَٱلَّذِينَ لَا يَشۡهَدُونَ ٱلزُّورَ وَإِذَا مَرُّواْ بِٱللَّغۡوِ مَرُّواْ كِرَامٗا

(Su ne) kuma waxanda ba sa halartar wuraren baxala, idan kuma suka wuce ta wurin aikin assha to sai su wuce suna masu mutunta kansu



Sura: Suratul Furqan

Aya : 73

وَٱلَّذِينَ إِذَا ذُكِّرُواْ بِـَٔايَٰتِ رَبِّهِمۡ لَمۡ يَخِرُّواْ عَلَيۡهَا صُمّٗا وَعُمۡيَانٗا

(Su ne) kuma waxanda idan aka yi musu wa’azi da ayoyin Ubangijinsu ba sa fuskantar su suna kurame kuma makafi



Sura: Suratul Furqan

Aya : 74

وَٱلَّذِينَ يَقُولُونَ رَبَّنَا هَبۡ لَنَا مِنۡ أَزۡوَٰجِنَا وَذُرِّيَّـٰتِنَا قُرَّةَ أَعۡيُنٖ وَٱجۡعَلۡنَا لِلۡمُتَّقِينَ إِمَامًا

(Su ne) kuma waxanda suke cewa: “Ya Ubangijinmu, Ka ba mu masu sanyaya mana zukata daga matayenmu da zuri’armu, kuma Ka sanya mu abin koyi ga masu taqawa



Sura: Suratul Furqan

Aya : 75

أُوْلَـٰٓئِكَ يُجۡزَوۡنَ ٱلۡغُرۡفَةَ بِمَا صَبَرُواْ وَيُلَقَّوۡنَ فِيهَا تَحِيَّةٗ وَسَلَٰمًا

Waxannan su ne ake saka wa da xakuna na Aljanna saboda haqurin da suka yi, za kuma a tare su a cikinta da gaisuwa da sallama



Sura: Suratul Furqan

Aya : 76

خَٰلِدِينَ فِيهَاۚ حَسُنَتۡ مُسۡتَقَرّٗا وَمُقَامٗا

Suna madawwama a cikinta. Matabbata da mazauni sun kyautata



Sura: Suratul Furqan

Aya : 77

قُلۡ مَا يَعۡبَؤُاْ بِكُمۡ رَبِّي لَوۡلَا دُعَآؤُكُمۡۖ فَقَدۡ كَذَّبۡتُمۡ فَسَوۡفَ يَكُونُ لِزَامَۢا

Ka ce: “Ba ruwan Ubangijina da ku in ba don ibadarku ba; to ga shi kun qaryata, to wannan (sakamakonsa) zai zama azaba ce mai xorewa[1].”


1- Watau ba domin bayinsa na gari waxanda suke bauta masa kuma suna roqon sa ba, da ba ruwansa da su domin sun qaryata Manzon Allah ().