Da sunan Allah(1) Mai rahama Mai jin qai.

Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, Tsira da aminci su tabbata ga Manzon Allah da alayensa da sahabbansa, da waxanda suka yi koyi da su har zuwa ranar Alqiyama.

Bayan haka:

Lalle Alqur’ani shi ne mu’ujiza ta har abada. Allah ya saukar da shi ga Annabi Muhammadu () ya kuma umarce shi da ya isar da shi ga mutane baki xaya. Muma kuma an umarce mu da mu isar da wannan saqo, domin faxarsa (): “Ku isar, ko da aya xaya ce daga gare ni”. Duk da kasancewar Alqur’ani an saukar da shi da harshen Larabci, to amma an shar’anta mana mu tarjama ma’anoninsa zuwa ga sauran harsunan duniya, har saqon Allah ya isa ga mutane baki xaya. Tare da cewa mun sani ba zai yiwu a tarjama Alqur’ani harafi bayan harafi zuwa wani harshe ba, domin harshen Larabci harshe na musamman, hakanan kuma yaren Alqur’ani yare ne na musamman, domin da shi ne Allah ya qalu-balanci qwararrun masana harshen Larabci da su kawo kamarsa, amma suka kasa kawowa.

Da jimawa Musulmi sun yi ta qoqarin tarjama ma’anonin Alqur’ani zuwa ga wasu harsuna, sai dai kuma da dama daga cikin waxannan tarjamomi da aka yi a gurvace suke ko kuma suna da rauni, ko kuma aiki ne na wani mutum guda, ko kuma wasu ne waxanda suka haxu suka yi tare, amma ba su bi wani fayyataccen tsari ba. Wannan ya jawo aka samu kurakurai wajen isar da saqon da Allah ya zuba a cikin Alqur’ani mai girma.

Saboda haka sai muka ga lalle mu kafa Cibiyar Nur International wadda za ta xauki gabarin tarjamar ma’anonin Alqur’ani zuwa harsunan duniya. Wannan Cibiya tana aiki ne da wani tsari na ilimi wajen zaven waxanda za su mata aikin tarjama. Wannan tsari yana jigo biyar. Jigon farko shi ne mai tarjama xaya wanda ya cika wasu siffoni na musamman, sannna a samu wani masanin ilimin addinin Musulunci ya yi bitar aikin, sannan kuma a samu wani masanin wannan harshen shi ma ya yi bita, sannan a nemi masu nazari daga masana ilimummuka daban-daban da za su yi alqalancin aikin a dukkan matakansa, tare da kuma bita da za a riqa yi lokaci bayan lokaci don inganta aikin. Wannan

duka zai gudana ne a qarqashin kulawar sashen ilimi wanda ya qunshi shehunan malamai masana.

Tsarin gudanar da tarjamar ya qunshi abubuwa kamar haka:

1. Tsayawa a kan tarjamar nassin Alqur’ani kalma da kalma ba tare da qari ko ragi ba, sai idan ya zamanto ba za a fahimci tarjamar ba sai an shigar da wani qarin bayani, to a nan sai a bi hanyoyi kamar haka:

a) Idan qarin kalma xaya ce ko biyu, to sai a sanya ta a cikin tarjamar a kuma shigar da ita tsakanin baka biyu ( ).

b) Idan bayanin yana da tsayo ana rubuta ne a hashiya qasan shafi.

2. Dogaro da hadisan Annbi () sahihai da maganganun sahabbai da manyan malamai wajen fahimtar ma’anar aya.

3. Komawa zuwa ga mahimman littattafan Tafsiri, kamar Tafsirin Xabari da na Ibnu Kasir da na Qurxubi da sauransu, domin fahimtar ma’anoni masu zurfi.

4. Rashin tarjama sunan (Allah) da rubuta shi kamar yadda ake furta shi a Larabci. Mun yi bayanin dalilin yin haka a hashiya mai lamba 1.

5. Tabbatar da ma’anonin siffofin Allah kamar yadda suka zo a Alqur’ani ba tare da yi musu tawili ba. Wajibi ne mai karatu ya sani cewa, siffofin Allah, kamar Hannu da Ji da Gani da Daidaito da Qarfi da makamantansu, ko da a lafazi sun yi kama da siffofin mutane, sai dai a haqiqarsu sun sava musu nesa ba kusa ba. Watau dai Allah yana da Hannu amma ba irin na mutane ba, kuma ba mu san qaqa Hannunsa yake ba. To haka lamarin yake ga duk siffofinsa (). Yana daga cikin wajiban aqida imani da duka siffofin Allah, da tabbatar su kamar yadda suke ba tare da wani hasashe a kansu ba, ko kwatance ko canza musu ma’anoni. Allah yana cewa: “Babu wani abu da ya yi kama da Shi, Shi Mai ji ne Mai gani ne”. [As-Shura, aya ta 11].

6. La’akari da tsarin zubin jumlolin Alqur’ani wajen gabatarwa da jinkirtarwa, gwargwadon yadda za su dace da qa’idojin harshen Hausa.

Yana daga cikin alfanon da wannan Tarjama ta kevanta da shi ga mai karatu:

1. Amafani da harshe mai sauqi wanda zai dace da duk masu karatu, tare da kula da fasaha da azancin magana.

2. Qarancin shigar da qare-qare a cikin tarjama hakan da qarancin hashiya, don mai karatu ya ji daxin karatu ba tare da an samu matsala ta fito da ma’ana ba.

3. Siffanta Allah da abin da ya siffanta kansa da shi, domin mai karatu ya san Ubangijinsa da ya halicce shi ya halicci halittu baki xaya, ya kuma san ta yaya zai bauta masa yadda ya dace.

4. Yi wa mai karatu bayanin dalilin halittar sa a bayan qasa da bayani yadda ya kamata ya gudanar da rayuwarsa. Da kuma yi masa bayanin qarshen sakamakon ayyukansa a duniya da lahira.

5. Daga qarshe, mun ba da muhimmanci ga kyan rubutu da girmansa da kyakkyawan tsari wajen zubin littafin da wallafi da kuma xab’insa, domin idan zubin abu ya yi kyau yana taimakawa wajen qara fito da kyan abin da ya qunsa.

Don haka, mai karatu, muna gabatar maka da wannan Tarjamar da fatan za ta amfanar da kai, kuma za ta amfane ka wajen fahimtar saqon Allah da fahimtar Musulunci da aiki da abin da ya zo da shi na alheri. Sannan muna qara nanata cewa, ga duk mai son ya fahimci Alqur’ani fahimta mai zurfi, to dole ne ya karance shi cikin harshen Larbaci, don haka muke ba da shawara ga kowane Musulmi da ya nemi ilimin sanin addinin Musulunci na gaskiya, kuma ya koyi harshen Larabci, domin harshe ne mai daxi, kuma mai sauqin koyo.

Daga qarshe muna miqa godiya mai tarin yawa ga duk waxanda suka ba da gudunmawa wajen samun nasarar wannan Tarjama, musamman Farfesa Zaid bn Umar Al-Ees, shugaban Cibiyar Bayyinat Domin Nazarin fannonin Alqur’ani. Kamar yadda muke miqa godiya ta musamman ga Dr. Muhammad Sani Umar Rijyar Lemo da abokan aikinsa, waxanda suka yi bitar aikin tare da shi, da duk wani wanda ya ba da wata gudunmawa don yaxa wannan aiki ga mutane.

Dukkan yabo da kirari sun tabbata ga Allah Ubangijin talikai.


(1) Allah: Shi ne Ubangiji Mahaliccin komai. Allah yana da sunaye da siffofi da dama, sai dai sunansa (Allah) suna ne da ya sha-banban da sauran sunaye, domin lafazin (Allah) suna ne na Zati, duka sauran sunaye da siffofin Ubangiji suna koma wa ne gare shi. Dalilin haka kuwa, saboda shi ba suna ne da aka tsago shi daga wata kalma ba. Kuma ba za a iya kiran wani mahaluki da shi ba, ba za a mayar da shi sunan mace ba ko a yi jam’insa. Ba wani harshe da zai iya ba da wani suna irinsa. Don haka ne muke rubuta shi kamar yadda ake furta shi da Larabci, ba mu tarjama shi zuwa Ubangiji ko Mahalicci ko wani suna makamancin wannan, domin duk kalmar da za a kawo, to za ta nuna wani vangare ne na ma’anar sunan Allah. Hakanan sunan Allah ya zama mai banbance tsakanin Musulmi da waxanda ba Musulmi ba, savanin da a ce an tarjama shi da sunan ubangiji, domin kowa ma yana da nasa ubangijin na qarya da yake bautawa, amma mu Musulmi muna bautawa Allah ne Xaya Tilo.